Gwamnatin Katsina Ta Haramta Amfani Da ’Yan Daba a Kamfen 2023 

Gwamnatin Katsina Ta Haramta Amfani Da ’Yan Daba a Kamfen 2023 

A kokarin tabbatar da zaben 2023 cikin aminci, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya sanya hannun kan dokar hana damawa da 'yan daba a gangamin zabe a fadin jiharsa, AIT ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana wannan ne ta bakin mai ba shi shawari kan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina, kuma ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da zaban shugabannin da suka dace a zaben da za yi. 
Ya kuma bayyana cewa, tunda wannan ne zaben karshe da za a yi a mulkin Masari, yana da kyau a yi shi cikin aminci domin kafa tarihi na gari a jihar. Hakazalika, ya ce gwamna Masari dattijon kasa ne, kuma zai tabbatar da zaman lafiya a jihar, musamman a kokarinsa na dawo da martabar jihar a matsayin kasa mai tarbar baki. 
Daga karshe ya shawarci 'yan siyasa da suke yiwa 'yan daba kallon 'ya'yansu kuma ya kamata su ba su wadataccen ilimi a madadin bata rayuwarsu ta hanyar mai dasu tsageru. Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula ta CCSO, Abdulrahman Abdullahi ya yaba da kokarin Masari na damawa da 'yan daba, tare da bayyana cewa hakan zai tabbatar da zabe na gari a Katsina.