Home Manyan Labaru Gwamnatin Kano ta ba da umarnin bincike kan mutuwar matar aure da...

Gwamnatin Kano ta ba da umarnin bincike kan mutuwar matar aure da likita ya manta almakashi a cikinta

4
0

Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wata matar aure mai suna Aishatu Umar, wadda ake zargin ta rasu sakamakon sakaci a aikin likitanci bayan an yi mata tiyata a asibitin Abubakar Imam.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Samira Suleiman, ta fitar a ranar Talata.

“Kwamitin Kula da Asibitocin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Babban Sakatare, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya lura da rahoton da ya tayar da hankula game da rasuwar Aishatu Umar.

“Muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalanta da masoyanta. Babban Sakatare ya bayar da umarnin a gaggauta gudanar da cikakken bincike kan zargin da aka yi a asibitin Abubakar Imam domin gano gaskiya da abin da ya faru,” in ji ta.

Hukumar ta tabbatar wa jama’a cewa binciken zai kasance a bayyane, ba tare da son zuciya ba, kuma cikin ƙwarewa, tare da ƙara da cewa za a ɗauki matakan da suka dace bisa ƙa’idoji idan aka tabbatar da wani sakaci.

Idan za iya tunawa cewa an rawaito marigayiya Aishatu Umar ta rasu ne bayan abin da iyalanta suka bayyana a matsayin zargin sakaci a aikin likitanci bayan an yi mata tiyata a asibitin.

A cewar wani ɗan uwa, Mohammed, wanda ya wallafa a shafin Facebook, marigayiya Aishatu, matar aure mai ‘ya’ya biyar, ta rasu da misalin ƙarfe 1 na dare a ranar Talata bayan ta sha fama da ciwon ciki mai tsanani tun bayan tiyatar da aka yi mata a watan Satumba na 2025.

“Ta fara korafin ciwon ciki mai tsanani wanda ya ci gaba har tsawon watanni. Ta sha wannan ciwo na tsawon watanni huɗu,” in ji Mohammed.

Ya yi zargin cewa duk da yawan komawarta asibitin, ma’aikatan lafiya suna ba ta magungunan rage zafi ne kawai su sallame ta ba tare da yin cikakken bincike ba.

Mohammed ya ƙara da cewa sai kwanaki biyu kacal kafin rasuwarta ne aka yi mata cikakkun gwaje-gwaje da hotunan bincike (scans), waɗanda suka nuna wai an bar almakashi guda biyu a cikin jikinta tun lokacin tiyatar watan Satumba.

“An fara shirye-shiryen yin gyaran tiyata, amma lokacin nata ya ƙare,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here