Gwamnatin Jigawa Ta Kawo Tsarin Ilmi Kyauta har Zuwa PhD Ga Mata

Gwamnatin Jigawa Ta Kawo Tsarin Ilmi Kyauta har Zuwa PhD Ga Mata


Gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta fito da tsarin ba mata damar yin karatu kyauta. Gwamnatin Jigawa ta fito tsarin ilimi kyauta ga mata ƴan asalin jihar tun daga matakin firamare har zuwa digirin digirgir (PhD) a makarantun gwamnati. 
Jaridar The Punch ta rahoto cewa kwamishinan ilmi mai zurfi na jihar Jigawa, Farfesa Isa Chamo, ya bayyana hakan. 
Wannan tsarin na musamman, wanda Gwamna Umar Namadi ke jagoranta, yana da nufin ƙarfafa mata ta hanyar ilimi ba tare da la’akari da fannin karatun da suka zaɓa ba. 
Kwamishinan ya bayyana cewa shirin zai yi tasiri sosai a rayuwar ɗalibai mata, rahoton Daily Post ya tabbatar. 
"Mun yi imanin cewa wannan shiri zai yi tasiri mai ɗorewa ga rayuwar ɗalibanmu mata. 
Wannan wani gagarumin mataki ne wajen tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata tare da ƙarfafa mata ta hanyar ilimi." 
"Ta hanyar samar da ilimi kyauta ga mata ƴan asalin jiha, gwamnatin Jigawa tana ba wa mata damar kula da rayuwarsu, yanke shawarwari masu kyau da kuma bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban al’ummominsu." - Farfesa Isa Chamo Kwamishinan ya bayyana fatan gwamnati na cewa wannan tsari zai jawo hankalin yara mata da yawa su ci gaba da neman ilimi, tare da tabbatar da cewa rashin kuɗi ba zai zama cikas ga burinsu ba.