Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu ya ƙara wa'adin mulki ga shugabannin ƙananan hukumomin jahar su 23 kamar yadda dokar ƙananan hukumomi da aka yiwa gyaran fuska a 2008 ta tanadar, ana iya karin wa'adi gare su.
Sai dai gwamnan bai bayyanawa al'ummar jiha yawan lokacin da ya ƙarawa Kantomomin ba, kuma abin da ya kamata ne a sanar a fili don shugabanni ne na jama'a.
Karin wa'adin zai baiwa hukumar zabe mallakar jiha damar shirya zaɓe a ƙananan hukumomi 23 da kansilolinsu 244.
Sakataren yada labarai na Gwamna Abubakar Bawa a bayanin da ya fitar ya ce gwamnan ya taya murna ga shugabannin rikon kan karin wa'adin.
Ya ba su tabbacin cigaba da goya musu baya su saukar da nauyin da aka daura musu.
Sakataren yada labarai na gwamnan bai ɗaga wayar wakilinmu ba da ya kira shi domin sanin lokacin da aka ƙara wa shugabannin ganin an ɓoye lokacin, abin da wasu ke ganin da akwai lauje cikin naɗi.