Gwamnan Sakkwato ga jami'an tsaro: Ku dauki Infoma da 'yan bindiga abu daya ne

Gwamnan Sakkwato ga jami'an tsaro: Ku dauki Infoma da 'yan bindiga abu daya ne
Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu ya shawarci jami'an tsaron Nijeriya da su dauki duk duk wani Infoma da yake bayar da kwarmato ga 'yan bindiga shi da 'yan bindigar abu daya ne don haka su rika daukar masu mataki kala daya.
Gwamna ya bayar da umarnin ne a ƙaramar hukumar Wurno da Rabah a lokacin da ya ziyarci kananan hukumomin a Litinin data gabata, domin jajanta masu kan harin 'yan bindiga da suke fama da shi.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta himmatu wurin ganin ta dakike harin 'yan bindiga ya yi kira ga mutane dake zaune a kauyukka su tona asirin duk wanda suka sani yana wannan muguwar ɗabi'a ga hukumar da ta dace domin yin bincike na adalci.
Gwamna Ahmad ya nuna takaicinsa kan wannan dabi'ar ta rashin kishin kasa da suka sanya kansu a ciki waton "bayar da kwarmato" saboda  dan abin da bai taka kara ya karya ba.
Ya gargadi mutane da su nemi sana'a ta halal domin cigaba da rayuwa mai inganci, ba wani Infoma da zai tsira a wannan sabon tsarin da aka fito da shi na kawar da 'yan bindiga a jiha.
"Mun himmantu na ganin sai mun zakulo wadan nan infoma da suka hana jama'armu zaman lafiya ko ta halin kaka.
"Don haka mu ke rokon jama'a da su bayar da hadin kai don dawo da zaman lafiya mai dorewa a jihar Sakkwato," ya kara da fadin.
Gwamnan ya yi kira ga limaman jumu'a da sauran lilamai da su yi wa'azi kan matsayar addini kan abin da ya shafi 'yan bindiga da Infoma da sauran aiyukkan barna.