Gwamnan Osun na PDP ya ayyana goyan bayansa ga Tinubu domin yin wa'adi na 2 a 2027

Gwamnan Osun na PDP ya ayyana goyan bayansa ga Tinubu domin yin wa'adi na 2 a 2027

Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun ya goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu don zaben 2027.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, gwamnan ya bayyana goyon bayan su ga Shugaba Tinubu domin sake tsayawa takara a 2027, yana bayyana shi a matsayin ɗan jihar da ya cancanta.

Sanarwar ta ce:

“Jiya na gana da jagororin jam'iyyar PDP  a Osogbo bayan makonni na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fadin Osun — daga sarakunan gargajiya da ma’aikatan gwamnati zuwa shugabannin kasuwa da ’yan jam’iyya a matakin ƙasa.

“Ina farin cikin sanar da matsayar da muka cimma:

“Zan ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar PDP, jam’iyyar da ta ba ni damar yin hidima ga mutanen Osun.

“An amince da ni gaba ɗaya a matsayin ɗan takarar PDP na wa’adin biyu a 2026 a Osun.

“PDP ita ce jam’iyya mafi shahara kuma mafi aminci a fadin Jihar Osun.

“Soyayya da goyon bayan mutanen Osun suna ci gaba da karfafa min guiwa. Tare za mu cigaba gaba.

“Jam’iyyarmu a Osun ta kuma amince da Shugaba Tinubu domin sake tsayawa takara a 2027, bisa kasancewar sa  a matsayin ɗan jiharmu mai alfahari.”