Gwamnan Kebbi Ya Nemi Bahasi Kan Janyewar Sojoji Kafin Sace ’Yan Matan Makaranta a Maga

Gwamnan Kebbi Ya Nemi Bahasi Kan Janyewar Sojoji Kafin Sace ’Yan Matan Makaranta a Maga

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bukaci rundunar sojin Najeriya ta bayyana dalilin da ya sa dakarunta suka janye daga Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati, Maga, kasa da awa guda kafin da wasu ’yan bindiga suka kai farmaki suka sace dalibai mata da dama.

Idris ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis yayin da yake karɓar tawagar kungiyar kwadago ta kasa (NLC) karkashin jagorancin shugabanta, Joe Ajaero, wadanda suka kai masa ziyarar ta’aziyya da goyon baya.

Gwamnan ya ce lamarin ya tayar masa da hankali matuka, musamman ganin cewa gwamnatin jihar ta riga ta tura bayanan sirri ga hukumomin tsaro tun kafin faruwar harin. A cewarsa, rahotanni sun nuna cewa sojojin sun bar wurin ne kimanin karfe uku na safe, yayin da maharan suka kai farmaki mintuna kadan bayan hakan.

Ya ce: “Mun mika bayanan sirri. Mun sanar da su barazanar. Don haka wa ya bayar da umarnin janye dakarun a wannan lokaci mai matukar hadari?” Idris ya tambaya tare da bukatar a gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa.

Haka kuma, gwamnan ya ce janyewar dakarun ya sabawa alkawarin da hukumomin tsaro suka bayar na karfafa tsaron makarantun da ke kan iyaka, musamman a yankunan da ’yan bindiga ke kai hare-hare akai-akai.

A yayin ziyarar, shugaban NLC, Joe Ajaero, ya nuna goyon bayan kungiyar ga gwamnati da iyalan ’yan matan da aka sace, tare da kira ga hukumomin tsaro na kasa da su dauki matakan da suka dace domin kubutar da su cikin gaggawa.

Lamarin sace daliban ya kara jawo fargaba da bacin rai a fadin kasar, domin kuwa ya sake jaddada matsalar hare-haren makarantun Arewa maso Yamma, duk da alkawurran gwamnati na karfafa tsaro a cibiyoyin ilimi.

Wannan sabon hari ya kara shiga jerin makamantansu da ke faruwa a yankin, inda hakkokin ’yan makaranta da tsaron su ke ci gaba da fuskantar barazana.