Gwamnan Bauchi ga Wike: Ba wanda ya isa ya kunna min wutar rikici a jiha

Gwamnan Bauchi ga Wike: Ba wanda ya isa ya kunna min wutar rikici a jiha

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ce babu wanda ya isa ya kunna wuta a Bauchi "saboda muna da isasshen ruwa na kashe wutar".

Ya fadi hakan ne yayin da ya karbi shugabannin jam'iyyar PDP na kasa a yau Talata.

Ya ce,  "Muna tare; ba wanda ya isa ya kunna wuta a Bauchi. Muna da isasshen ruwa na kashe wutar, ko da abokina ma da ya fadi hakan saboda yana cikin bacin rai. Amma abin bai shafi alaka ta kashin kai ba. Abokina, abokina ne, kuma aikina aiki na ne. Shugabanci shugabanci ne".

Wannan ne karo na farko da gwamnan ya mayar da martani ga barazanar ta Nyesome Wike, ministan Abuja, wanda ya zargi Gwanonin PDP da shiga rikicin da ya shafi jam'iyyar a jihar Rivers.

A wani taro da Gwamnonin PDP suka yi a watan Agusta, sun ayyana goyan bayansu ga Gwamna Siminalayi Fubara a rikicin da suke yi da Wike kan jagorantar jam'iyyar.