Gwamna Zulum Ya Raba N275m Ga 'Yan Gudun Hijira 90,000 A Monguno

Gwamna Zulum Ya Raba N275m Ga 'Yan Gudun Hijira 90,000 A Monguno
 

 

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya raba kudade kimanin Naira miliyan 275,000,000 tare da raba buhunan hatsi, da suturun sawa ga magidanta kimanin 90,000 da ke gudun hijira a Monguno.

 
Gwamna  Zulum tsawon shekaru uku da ya yi akan Mulki yana irin ya hakan wadda wani bangare ne na kokarin daban-daban ya ke  yi na don kara wa al’ummar da hare-haren Boko Haram ya shafa karfin gwiwa ta hanyar tallafa musu da abin dogaro da kai, a sannu a hankali suke wucewa zuwa noma, da matsakaitan sana'o'i domin a karshe su biya bukatun kansu.
 
Tallafin kudin ya kuma kasance wani ingantaccen kayan aiki don yaki da ikon Boko Haram na daukar ’yan leken asiri daga talakawa da marasa galihu, ta hanyar bai wa wasu mazauna yankin kudin da ya kai Naira 5,000 a matsayin tallafin kudi.
 
Gwamna Zulum, tare da babban mai shigar da kara na majalisar wakilai, Barr.  Mohammed Tahir Monguno ya yi tattaki ne daga Maiduguri inda ya kwana a garin Mafa, kuma ya isa Monguno da safiyar Juma'a domin fara ayyukan jin kai.
 
Monguno ya karbi bakuncin ‘yan gudun hijirar da suka fito daga kananan hukumomi kusan biyar da ke gefen tafkin Chadi, da kuma ‘yan gudun hijirar da suka dawo daga Jamhuriyar Nijar bayan sun tsere daga hare-haren Boko Haram a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014.