Gwamna Tambuwal Ya Zama  Shugaban Kungiyar Gwamonin Nijeriya

Gwamna Tambuwal Ya Zama  Shugaban Kungiyar Gwamonin Nijeriya

 

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya maye gurbin takwaransa na jihar Ekiti, Kayode Fayemi a shugabancin kungiyar gwamnonin Najeriya, Punch ta ruwaito. 

Tambuwal ya karbi shugabancin ne a yau Alhamis 22 ga watan Satumba a taron majalisar tattalin arzikin kasa da aka yi a Aso Rock Villa, Abuja, inda Fayemi ya mika masa sandar mukamin. 
Sanarwar da daraktan yada labarai na NGF, Abdulrazaque Bello Barkindo ya fitar ta ce "Tambuwal ya yi aiki tukuru cikin gaskiya da aminci a lokacin da yake mataimakin shugaban kungiyar karkashin shugabancin Dr Fayemi na shekaru hudu." 
Hakazalika, sanarwar ta ce, Tambuwal zai rike mukamin ne har zuwa watan Mayun 2023, lokacin da za a sake gudanar da zabe sahihi na kungiyar, rahoton Vanguard. 
Majiya ta ruwaito cewa, a kwanan nan ne aka zabi Fayemi a matsayin shugaban kungiyar gwamnatocin shiyya da kasashe a Saidia ta jihar Casablanca a kasar Morrocco. 
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya taya Tambuwal murna, ya kuma yiwa gwamna Fayemi addu'ar nasara a ayyukansa na kasa Najeriya da ma wanda ya samu a kasar waje.