Gwamna Tambuwal Ya Yi Murabus Kan Shugabancin Da Yake Yi

Gwamna Tambuwal Ya Yi Murabus Kan Shugabancin Da Yake Yi

 

Shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi murabus daga kujerarsa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sakkwato daga arewacin Najeriya, ya sanar da murabus ɗinsa ne a wurin taron kwamitin amintattu (BoT) dake gudana yanzu haka a Abuja. 

Tun farko manema labarai sun  kawo muku rahoton cewa shugaban BoT na ƙasa, Sanata Walid Jibrin, ya sauka daga kan muƙaminsa, lamarin da ya jefa kujerar Tambuwal cikin rashin tabbas.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa matakin Sanata Jibrin zai rinjayi gwamna Tambuwal ya sauka daga kujerar shugaban gwamnonin PDP domin ya share hanyar komawar kujerar kudancin Najeriya.

Jam'iyyar PDP ta tsunduma cikin rikici tun bayan ayyana Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da kuma zaɓo gwamna Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa. Tsagin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya cigaba da nanata bukatarsu cewa ya zama wajibi shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorcia Ayu, ya bar kujerarsa a wani ɓangaren kokarin sulhu. 

Sai dai a halin yanzu, masu ruwa da tsakin jam'iyya musamman 'yan arewa sun rinjayar da cewa shugaban BoT da Gwamna Aminu Tambuwal, su yi murabus daga muƙamansu domin a baiwa kudu hakan kuma aka yi, har Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya karbi ragamar shugabancin kungiyar gwamnonin PDP na Nijeriya.