Gwamna Raɗɗa ya ƙara tallafin kuɗi daga dubu 10 zuwa 15 ga ma'aikatan jihar Katsina
Gwamnan jihar Katsina Dikko Raɗɗa, ya mayar da kuɗin tallafin naira dubu 10 ga ma'aikatan jihar da dubu 5 ga yan fansho zuwa dubu 15 don rage masu radadin tsadar rayuwa da cire tallafin man fetur ya haifar.
Hakazalika, Gwamna Raɗɗa, ya yi karin dubu 5 ga ƴan fansho zuwa dubu 10 domin rage masu radadin tsadar rayuwa.
Gwamnan ya Sanya kudin ne bayan da gwamnatin tarayya ta shawarci Gwamnoni da su tallafawa ma'aikatansu da dubu 25 a kowane wata don rage radadin cire tallafin man fetur.
Wasu jihohi sun ba da kudin in da wasu har yanzu ko maganar ba su yi ba balle ma'aikatan sun yi tsammani an barsu suna Shan bakar wahala.
managarciya