Giwaye Na Yin Barazana Ga Rayuwar Al'ummar Jihar Borno
Al'ummar garin Rann a karamar hukumar Kala Balge da ke Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya sun sami kansu cikin fuskantar barazanar da giwaye ke musu ta wajen barnata musu amfanin gonar da suke nomawa a cikin shekaru biyu.
Wannan yanki na.Rann yanki ne da tun tunin al'ummomin Sa ke fama da rikicin Boko Haram, halin da mazauna kauyukan Rann ke ciki ya dauki hankulan jama'a ganin yadda sana'arsu ta noma ta shiga tsaka mai wuya sakamakon barnar da wadannan manya-manyan dabbobi ke musu,
“Mu manoma ne; mun dogara da abin da muke noma don mu tsira,” in ji Ajid, wani mazaunin Rann.
“Bayan da Boko Haram ta raba mu da muhallanmu, yanzu kuma muna fuskantar giwaye da ke lalata gonakinmu wadda Mun dade muna shigar da korafin mu, amma har zuwa yau din nan da nake magana babu wanda ya nuna sha’awar taimaka mana, duk da kasancewar shugabanninmu suna sane."
A cewar Malam Musa wani manomi a Rann kusan dukannin Koke-koken bisa ga dukannin alamu an Yi kunnen uwar shegu da shi lamarin da ya sa muka ji shiru da roko da muki na daukar matakin kawo mana dauki akan wannna hali da muke daga gwamnati wadda da alama ba a ji ba.
Wata majiya da ke garin na Rann na bayyanawa manema labarai cewar yanzu haka mazauna garin Rann sun tsaya tsayin daka kan matsayar da suke da shi na ganin an shawo kan matsalar da suke ciki musamman ta wajen yin matsin lamba ga shugabannin Jihar don ganin an kawo musu dauki.
"Muna kira ga hukumomi da su dauki matakin gaggawa kafin lokaci ya kure, wadda tasirin wadannan hare-haren giwaye na iya haifar da mummunan sakamako da kan iya haifar mana da karancin abinci da kuma kara wahalhalu ga al'ummarmu." In ji Malam Mousa.
Kalubalen da al’ummar garin Rann ke fuskanta ya ta’allaka ne da irin yadda Yankin ke da sarkakiya wanda ke kawo cikas ga shiga tsakani na gwamnati. Sakamakon haka, kauyen ya tsinci kansa a cikin wani mawuyacin hali na matsalar noma, inda ake ganin karancin abinci kan iya yin kamari.
Dangane da neman agajin mutanen kauyen, ya zama wajibi hukumomi su yi amsa kiran nasu tare da daukar matakin gaggawa akai don shawo kan wannan matsala kasancewar rayuwar mutanen Rann ta rataya a wuyansu, kuma ana bukatar daukar kwararan matakai don hana kara yiwuwar haifar da asara da wahala ga dukiyar al'ummar Yankin inji Ahmed Shehu wani Mai fafutukar neman 'yancin farar hula.
" A cewar Ahmed Shehu Mutanen Rann na fuskantar wannan annoba ta giwaye bayan bala'in Boko Haram da suke fama da shi wadda ya dace cikin gaggawa gwamnatoci su kula da halin da suke ciki don daukar matakin fitar da su daga cikin wannna yanayin."
“Yanzu ya zama wajibi ga masu rike da madafun iko su tashi tsaye wajen gudanar da wannan gagarumin aiki tare da shimfida hanyoyin rayuwa ga al’ummar da ke cikin matsananciyar bukata, kuma lokaci ya yi da ya kamata a dauki mataki a yanzu, kafin barnar da wadannan giwaye suka yi ya zama bala’i da ba za a iya shawo kan sa ba ga mutanen Rann.”
managarciya