Gidauniyar Usman Kesoje ta bayar da tallafin kayan karatu da suka hada da tufafin makaranra da littafai ga dalibbai maza 600 da mata 400 daga makarantu 10 dake karamar hukumar Shagari a Sakkwato.
A sadaukarwar da yake da ita don ganin ilmi ya samu cigaba musamman koyo da koyarwa Usman Abubakar Kesoje a karkashin gidauniyarsa ya tallafawa makaranta 10 a Shagari.
A lokacin rabon kayan Sakataren ilmi na Shagari, mataimakinsa Muhammad A, Muhammad ne ya wakilce shi, ya nuna farincikinsa da tallafin gidauniyar.
Ya bayyana tallafin ya zo kan lokaci zai amfani yaran a dukkan makarantun.
Haka ma ya yi kira ga masu hali da ke son cigaba da kungiyoyi su yi koyi da Kesoje domin samar ingantaccen ilmi abu ne da ya rataya kan kowa.
Wakilin gidauniyar Malam Bashiru Kesoje ya tabbatar da kudirin Usman Abubakar na son cigaban mutanen yankinsa a haujin ilmi kan haka gidauniyar za ta ci gaba da tallafawa shiraruwan ilmi da za su bunkasa koyo da zai sai mutane su rika zuwa makaranta.





