Gangamin Tarbon Tambuwal Tsugunne Bata ƙare Ba 'Sakkwato Sai Wali'

Gangamin Tarbon Tambuwal Tsugunne Bata ƙare Ba 'Sakkwato Sai Wali'

Tun bayan kammala zaben fitar da gwani na jam'iyar PDP a Assabar data gabata Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal bai koma jihar sa ba a yau Jumu'a in da aka shirya masa gangami na musamman domin tarbarsa bayan namijin kokarin da ya yi a Abuja.

Gangamin tarbon ya fito da wani abu da ke nuna tsugune bata kare ba a tafiyar siyasar jam'iyar PDP in da wasu matasa magoya bayan Mataimakin Gwamna Maniru Muhammad Dan'iya suka yi ta rera salon 'sai Wali'
Wannan halayyar ta nuna rashin gamsuwa karara da zaben da gwamna ya yi na mika takarar gwamna ga tsohon sakataren gwamnatinsa Malam Sa'idu Umar.
Jam'iyar PDP na bukatar ta yi wa tufkar hanci domin bai dace magoya bayan jam'iya daya su rika nuna wanda suke so a tsayar, shi ne kawai zabinsu sabawa zai sa su yi tawaye ko nuna rashin biyayya.
Matasan sun rika fadin sai Wali tun a lokacin da ake jawabi ga magoya bayan PDP jim kadan da tarbo Tambuwal sun yi ta wannan har sai lokacin da ya bar gidan gwamnati bayan ganawa da wasu muhimman mutane.