Ganduje Ya Gabatar Da Kasafin Kudi na Biliyan 196.3 A 2022

Daftarin da aka yi wa lakabi da “Kasafin karo, karin karsashi da cigaba” (Budget for Consolidation and Prosperity)  Biliyan 107.8  don gabatar da manyan ayyuka da kuma Biliyan 88.4  don gudanar da ayyukan yau da kullum. A jawabinsa, Gwamnan ya fara da mika gaisuwa ga shugaban majalisar dokokin, Honarabul, Hamisu Ibrahim chidari da sauran yan majalisa sannan ya gabatar da yadda aka kashe kasafin kudin shekarar data wuce da kuma bayanin yadda za'a kashe kasafin kudin na shekarar 2022 dalla-dalla.

Ganduje Ya Gabatar Da Kasafin Kudi na Biliyan 196.3 A 2022

Ganduje Ya Gabatar Da Kasafin Kudi na Biliyan 196.3 A 2022

 

Gwamnan Jihar Kano, Dakta  Abdullahi Umar Ganduje, ya gabatar da daftarin kasafin kudin Jihar Kano wanda ya cimma  naira biliyan 196.3 na shekarar 2022 ga majalisar dokokin Jihar Kano.

Daftarin da aka yi wa lakabi da “Kasafin karo, karin karsashi da cigaba” (Budget for Consolidation and Prosperity)  Biliyan 107.8  don gabatar da manyan ayyuka da kuma Biliyan 88.4  don gudanar da ayyukan yau da kullum.

A jawabinsa, Gwamnan ya fara da mika gaisuwa ga shugaban majalisar dokokin, Honarabul, Hamisu Ibrahim chidari da sauran yan majalisa sannan ya gabatar da yadda aka kashe kasafin kudin shekarar data wuce da kuma bayanin yadda za'a kashe kasafin kudin na shekarar 2022 dalla-dalla.

Gwamnan ya samu rakiyar Mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da sauran 'yan majalisar zartarwa na jiha, Shugabannin kananan hukumomi da sauran jami'an gwamnati.