Gamayyar cibiyoyin mahaddata Alkur'ani ta karrama tsohon Gwamnan Kano Ganduje 

Gamayyar cibiyoyin mahaddata Alkur'ani ta karrama tsohon Gwamnan Kano Ganduje 


Daga Wakilinmu.    


         
Gamayar Cibiyoyin Mahaddata Alƙur'ani ta Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Gwani Yusuf Hamza Yusuf, Garkuwar Hafizai, ta sanar da al'ummar musulmi musamman mahaddatan Alƙur'ani Mai Girma cewa, wannan cibiyar ta bai wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje shaidar karramawa tare da naɗa shi muƙamin, Khadimul Huffazul Qur’an, duba da irin cigaban da yake bai wa ƙungiyoyin addinin Musulunci.

Ƙungiyar ta kafa hujja da irin yadda tsohon Gwamnan kuma tsohon shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, yake gina masallatai da makarantu da kuma babban aikin alherin da yake yi na musuluntar da Maguzawa, wanda ya shafe fiye da shekaru 20 yana yi, a ƙarƙashin Gidauniyarsa ta GANDUJE FOUNDATION. 

Sannan harwayau, ya shafe tsawon shekaru yana ba da kujerun Umra da Hajji, da kuma ba da tallafi ga malamai da basu ababen hawa, don sauƙaƙa musu ziyarce-ziyarce.

Ƙungiyar ta ce, wannan naɗi an yi shi ne bisa amincewar dukkan shugabannin rassan ƙungiyar na jihohi 36 haɗi da Abuja.

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da wasu mutane dake son saka siyasa a harkar addini, inda ta yi kira ga magoya bayan ta da su cigaba da biyayya da kuma addu'a ga shugabannin su, da zaman lafiyar ƙasa bakiɗaya.