Gadauniyar Dangote ta rabawa kungiyar ƴan Jarida tallafin Shinkafa

Gadauniyar Dangote ta rabawa kungiyar ƴan Jarida tallafin Shinkafa

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

Gidauniyar Dangote ta baiwa kungiyar ƴan Jaridu ta kasa wato  (Arewa Online journalist Forum)  tallafin Shinkafa don rage raɗaɗi a wannan watan na Ramadan mai alfarma. 

Babbar manajan daraktan Kasuwancin Kamfanin Dangote, Hajiya Fatima Aliko Dangote ce ta dauki nauyi wannan tallafin domin su ma yan Jaridun su amfana da tallafin kamar yadda ake cigaba da rabawa a kasa baki daya,  

Hajiya Fatima dai ba bakuwa ba ce wajen tallafawa al'ummar arewa da ma ƙasa baki daya, inda ta gaji  kyawawan hali irin na  mahaifinta Alhaji Aliko Dangote, 

Shugaban Kungiyar yan jaridu ta ta kafafen sadarwa wato (Arewa Online journalist Forum) Malam  Barrah Almadany ya mika sakon godiya ga uwar marayu Hajiya Fatima Aliko Dangote wajen yadda ta tsaya tsayin daka wajen tallafawa mabukata da kayan abinci a wannan wata na Ramadan. 

Kazalika, Almadany ya bukaci masu hannu da shuni da suyi koyi da irin  halaye na Hajiya Fatima Aliko Dangote wajen taimakawa mabukata idan halin haka ya samu  don rage raɗaɗi ga ƴan kasa.