Funkason Abincin Mai Ban Al'ajabi Ga Al'ummar Hausawa
Da fari za ki dauko fulawarki ki tankade ta sannan ki dauko garin alkama ita ma ki tankadeta, amma za ki iya yin na Alkama zalla idan kin fi son haka, idan na rabin kwano zaki yi sai ki saka fulawa gwangwani hudu,garin Alkama gwangwani hudu idan kina bukatar garin wake sai ki saka wake gwangwani biyu, amfanin saka waken zai kara mishi dadi laushi da kamshi, amma idan bakya ra’ayi to karki saka, sai ki dauko yist dinki kamar cokalin cin abinci daya, sai ki saka a ciki sannan ki zo ki kwaba su da ruwan zafi, ki kwaba shi da tauri , amma ba kamar taurin cin-cin ba, kamar dai kwabin fanke sai ki rufe da marfi mai nauyi sai ki kai shi gurin da zai yi saurin kumburowa, idan ya kumburo sai ki dauko shi ki buga shi sosai, sai ki diga ruwan kanwa kadan gudun kar ya yi tsami, sai ki dora sa a wuta idan yayi zafi sai ki dinga gutsuro kullum kina fadadawa da bayan mara, ko bayan faranti sai ki huda shi da yatsanki, sannan ki fara soya shi idan wannan barin ya yi sai ki juya wani bari sai kin ga yayi ja alamun ya soyu sai ki kwashe haka zaki yi ta yi har ki kammala.
FUNKASO
Aisha Basheer Tambuwal
Barka da wannan lokacin uwar gida da amarya harma da ‘yanmata masu bibiyar wannan shafi na GIRKE GIRKE, har wa yau dai muna ci gaba da kawo muku girke-girkenmu na gargajiya, a yau ma na zo muku da yanda ake ha]in FUNKASO, idan zaki hada wannan FUNKASO zaki tanadi>>>>>>>>
- Fulawa
- Alkama
- Wake idan kina bukata
- Yist
- Kanwa
- Mai
- Ruwa
Da fari za ki dauko fulawarki ki tankade ta sannan ki dauko garin alkama ita ma ki tankadeta, amma za ki iya yin na Alkama zalla idan kin fi son haka, idan na rabin kwano zaki yi sai ki saka fulawa gwangwani hudu,garin Alkama gwangwani hudu idan kina bukatar garin wake sai ki saka wake gwangwani biyu, amfanin saka waken zai kara mishi dadi laushi da kamshi, amma idan bakya ra’ayi to karki saka, sai ki dauko yist dinki kamar cokalin cin abinci daya, sai ki saka a ciki sannan ki zo ki kwaba su da ruwan zafi, ki kwaba shi da tauri , amma ba kamar taurin cin-cin ba, kamar dai kwabin fanke sai ki rufe da marfi mai nauyi sai ki kai shi gurin da zai yi saurin kumburowa, idan ya kumburo sai ki dauko shi ki buga shi sosai, sai ki diga ruwan kanwa kadan gudun kar ya yi tsami, sai ki dora sa a wuta idan yayi zafi sai ki dinga gutsuro kullum kina fadadawa da bayan mara, ko bayan faranti sai ki huda shi da yatsanki, sannan ki fara soya shi idan wannan barin ya yi sai ki juya wani bari sai kin ga yayi ja alamun ya soyu sai ki kwashe haka zaki yi ta yi har ki kammala.
Za ki iyacin wannan FUNKASON da farfesu ko da miyar taushe, yayin da mai gidanki yayi tafiya za ki iya tarbarsa da shi, za ki matu}ar burge shi.
managarciya