Fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa ta hanyar silhu shi ne  alheri  ga PDP---Tambuwal

Fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa ta hanyar silhu shi ne  alheri  ga PDP---Tambuwal

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya ce fitar da ɗan takarar shugaban kasa ta hanyar maslaha a zaɓen 2023 alheri ne ga jam'iyyar PDP.

Tambuwal, wanda yana ɗaya daga cikin masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zanta wa da manema labarai jim kadan bayan mika fom ɗin tsayawa da kuma nuna sha’awarsa ta tsaya wa takara a zaɓen shugaban kasa a Abuja a jiya Talata.

Tambuwal, wanda ya samu wakilcin Nicholas Msheliza, ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa tsarin maslaha wajen fitar da ɗan takarar zai taimaka masa.

“maslhaha aba ce mai kyau. Alheri ne ga jam'iyyar. Addu'ar mu, ina tunanin ita ce maslahar za ta  amfanar da ni.

"Ya zuwa yanzu, ni ne a sahun gaba, tunaninmu, addu'armu da fatanmu shine yarjejeniya ta tafi ta hanya ta."

Msheliza, wanda ya ce Tambuwal ya ba da goyon baya a duk fadin kasar, ya nuna farin cikinsa kan yadda ya samu karbuwa a tsakanin 'yan jam'iyyar PDP a fadin kasar, wanda ya bayyana a matsayin mai karfin gaske da karfafa gwiwa.

Ya kara da cewa Tambuwal zai ci gaba da ziyarar tuntubar sa a fadin kasar nan.