Ficewar Atiku ba za ta yi wa PDP wata illa ba –Gwamna Makinde
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce ficewar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar daga PDP, ba za ta haifar da wata matsala ga jam’iyyar ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa Atiku ya fice daga jam’iyyar PDP a jihar Adamawa a yau Laraba.
Makinde, wanda ya kasance babban bako mai jawabi a wani taron bitar ilimi domin bikin cika shekaru 10 da naɗin Oba Aladetoyinbo Aladelusi, Deji na Akure, ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a yau Laraba a Akure.
“Ina ganin hakan ba zai yi wa PDP wata illa ba. PDP wata cibiya ce, kuma kowa na da ‘yancin shiga da fita,” in ji shi.
managarciya