Fatattakar 'Yan Bindiga A Yankin Sakkwato: Tambuwal Ya Yaba Kokarin Sojojin Nijeriya

Fatattakar 'Yan Bindiga A Yankin Sakkwato: Tambuwal Ya Yaba Kokarin Sojojin Nijeriya

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yaba kokarin sojojin Nijeriya kan fatattakar 'yan bindiga da suke yi a yankin Sakkwato ta gabas.

A wani bayani da Gwamnan ya fitar  ya bayyana cewa a madadin gwamnati da jama'ar Sakkwato suna jinjinawa jami'an tsaro masu kishin kasa kan nasarar da suke samu ga barayin daji dake addabar wani yankin na Sakkwato musamman Sakkwato ta gabas da ta yi iyaka da Zamfara da jamhuriyar Nijar.

Ya ce Haka ma yaba kan hadin kan da aka samu a tsakanin jami'an tsaron shi ne silar samun nasara a farkamakin da aka kai wa 'yan bindigar, "Ina kira gare su da su daure da hakan su yi aiki tare da 'yan kasa masu biyar doka a cikin al'umma."
Ya ce shi kansa da mutanen jiha suna tare da jami'an tsaron da yi masu addu'ar samun nasara daga wurin Allah 'da ba ku tabbacin goyon baya har zuwa lokacin da za a mayar da zaman lafiya a jiha da kasa baki daya'.