#EndBadGovernance: Amnesty International Ta Yi Tir Da Kama Matasa 81 a Sokoto

#EndBadGovernance: Amnesty International Ta Yi Tir Da Kama Matasa 81 a Sokoto

 

Ƙungiyar kare haƙƙin Ɗan Adam ta Duniya Amnesty International ta yi tir da kama matasa 81 da 'yan sanda suka yi a jihar Sakkwato kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta rahoto.

Jaridar ta ce ƙungiyar ta yi alawadai da hukumar 'yan sanda, da ta kama matasan a lokacin da suke zanga-zangar lumana kan matsalar yunwa a jihar Sakkwato.

Jaridar ta kawo cewa a ranar Jumu'a bayani ya nuna mutum 21 suka rasu an kama mutum 1,154 jami'an tsaro suka kama kan zanga-zanga da ake yi a ƙasa cikin kwana biyu, ta #EndBadGovernance.

A Assabar hukumar 'yan sandan Sakkwato ta ce ta ƙara kama wasu matasa 21 bayan na farkon kan zargin saɓa doka a lokacin zanga-zangar.