EFCC za ta tuhumi ministoci 8 na tsohuwar  gwamnatin Buhari

EFCC za ta tuhumi ministoci 8 na tsohuwar  gwamnatin Buhari

Ministocin gwamnatin Buhari 8 za su fuskanci tuhume-tuhume  daga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC.

Jaridar Daily trust ta ce tuni hukumar ta EFCC ta fara da wasu daga cikin ministocin irin su; Pauline Tallen ministar mata da kuma tsohon ministan lantarki Injiniya Saleh Mamman da tsohon Ministan yan sanda Maigari Dingyadi.

A cikin makon nan wani labari ya karade shafukan sada zumunta na zamani da ke cewa hukumar ta EFCC ta gayyaci ministan Sufurin jiragen sama na waccen gwamnatin Sanata Hadi Sirika sai dai ya musanta cewa babu wata gayyata da ya samu daga hukumar ta EFCC.

Haka ma tsohon ministan Shari'a Abubakar Malami ya musanta maganar da ake yadawa ya gudu  ya bar kasar.