EFCC Ta Shawarci Dalibai Su Hada Gwiwa A Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

EFCC Ta Shawarci Dalibai Su Hada Gwiwa A Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ranar Alhamis 3 ga watan Maris, 2022, ya yi kira ga daliban kasarnan da su daina korafi su zo a hadu a yaki cin hancin da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Bawa wanda ya samu wakilcin shugabn sashen hulda da jama’a na hukumar Wilson Uwujaren ya yi kiran ne lokacin da daliban sashen shari’a na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria suka ziyarci hukumar. Inda ya shawarce da su kauracewa laifuka masu alaka da intanet.

Ya kuma yi kira garesu da su isar da sakon hukumar na yaki da cin hanci da  rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa zuwa ga al’ummar su  sannan su zama abin koyi na gari.

 A jawabin sa akan rawar da lauyoyi zasu taka wajen yaki da cin hanci da rashawa, shugaban sashen kula da ‘yanci da fadin ra’ayi na hukumar, Johnson Ojogbane ya ce, matsayin da mukasami kan mu a kasar nan yansu ill ace ta cin hanci da rashawa.

Ya bayyana musu cewa suna da rawa da zasu taka sosai wajen ci gaban kasar su, da al’ummar su da ma kansu.

Alvan Gurumma, wani jami’in hukumar EFCC ya bayyanawa daliban cewa, hukumar na aiki karkashin sashen doka na ACJA 2015.

Shugaban tawagar daliban, Yakubu Muhammed ya mika godiya ga hukumar da damar da suka samu inda ya bayyana cewa za su yi amfani da ilimin da suka samu wajen ilmantar da al’ummar su.