Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Babban Mai Binciken kudaden kananan hukumomin jihar Yobe (Yobe LGA Auditor General), Alhaji Idris Yahaya ya fada komar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Karbar Rashawa ta Nijeriya (EFCC) bisa zargin yin rub-da-ciki da dukiyar al'ummar tare da gurfanar dashi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu.
Da take sauraron karar, Mai shari’a Fadima Murtala Aminu ta Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu a jihar Yobe ta bayar da umarnin kwace wasu kadarori mallakin Alhaji Idris Yahaya 11 na wucin-gadi, wadanda suka kunshi gidaje, shaguna da filaye a birnin Damaturu.
Mai shari'ar ta bayar da wannan umarnin ne a ranar Laraba, 21 ga Satumban 2022, biyo bayan takardar karar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) dake shiyar Maiduguri ta shigar tana neman a kwace kadarorin na wucin gadi.
Lauyan Hukumar EFCC, Mukhtar Ali Ahmed, ya shaida wa kotun cewa Yahaya ya mallaki wasu kadarorin da ake zargin ba na halas ba ne, tare da aikata laifin karkata kudaden al'umma zuwa aljihunsa, sannan da cin amanar ofishin da aka damka masa da almuddahana da kudi, a rahoton koken da aka kai wa Hukumar su.
Lauya Ali Ahmed ya kara da cewa, wanda ya tsegunta wa Hukumar ayyukan almuddahanan ya zargin cewa wanda ake tuhumar da cewa ya arzuta kansa ne ta hanyar sanya ma’aikatan bogi a cikin jerin ma'aikatan kananan hukumomin jihar Yobe wanda ta wannan mummunan aika-aikar ya tara dukiya da kadarorin da ya mallaka.
“Har wala yau, binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya kamfaci makudan kudaden tare da karkatar dasu zuwa kansa daga asusun kananan hukumomin jihar Yobe, ya kuma mallaki wadannan kadarori ba bisa ka’ida ba."
Wadannan kadarorin sun kunshi: Farsawa Plaza da ke daura da First Bank, kan titin Gashua, Mega Plaza daura da Babban Bankin Najeriya (CBN), kan titin Gujba, Rukunin Gidaje 20 masu dakuna guda hudu, da masu dakuna guda biyu da falo, da ke daura da Babban Bankin Najeriya (CBN) kan titin Gujba, duk a cikin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Bugu da kari kuma, wakilinmu a jihar Yobe ya yi kokarin jin ta bakin Babban Mai Binciken Kudin kananan hukumomin jihar, Alhaji Idris Yahaya abin ya ci tura- har lokacin kammala wannan rahoton.