Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta sake dawo da binciken da ake yi wa wasu tsofaffin gwamnonin jihohi a Najeriya.
Binciken ya shafi tsofaffin gwamnoni 13 da kuma wasu wadanda suka rike mukaman ministoci kamar yadda Punch ta rahoto.
Zargin rashin gaskiya da ke kan wadannan manya ya kai N853.8bn.
Ana tunanin an yi gaba da N772.2bn daga asusun jihohin kawai.
Ana zargin ragowar N81.6bn da EFCC ta ke bincike sun yi kafa ne daga ma’aikatar jin kai da yaki da talauci a karkashin ministoci biyu.
Akwai wasu $2.2bn da ake zargin sun bace ta hanyar wawura a lokacin da Sambo Dasuki yake ba shugaban kasa shawara a kan tsaro.
An fitar da dalolin da sunan sayen makamai, amma aka karkatar da su.
Binciken da kwamiti ya yi ya jefa ‘yan siyasa da sojoji a matsala.
1. Bello Matawalle – N70bn
2. Kayode Fayemi – N4bn
3. Ayo Fayose – N9.6bn
4. Ken Nnamani – N5.3bn
5. Sullivan Chime – N450m
6. Abdullahi Adamu – N15bn
7. Rabiu Kwakwanso – N10bn
8. Theodore Orji – N100bn
9. Danjuma Goje – N5bn
10. Aliyu Wammako – N15bn
11. Timipre Sylva – N19.2bn
12. Sule Lamido – N1.2bn
13. Peter Odili – N100bn





