Duk Wanda Ya Ci Zabe Shi Zan Mika Wa Mulki a 2023, Inji Buhari a Filin Gangamin APC

Duk Wanda Ya Ci Zabe Shi Zan Mika Wa Mulki a 2023, Inji Buhari a Filin Gangamin APC

Buhari ya yi alkawali kan zaben 2023 ga duk wanda ya samu nasara


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, zai tabbatar duk wanda ya lashe zaben 2023 daga kowace jam'iyya ce ya samu 'yancin hawa kujerar shugaban kasa. Buhari ya ce, babu dan takarar da zai lashe zabe kana a tauye masa hakkinsa saboda wani dalili. 
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata 15 ga watan Nuwamba a filin wasa na Gbong Gwom yayin kaddamar da kamfen na jam'iyyar APC. 
"Babu wanda zai ci zabe sannan a hana shi hakkinsa, ba tare da la'akari da jam'iyyar da suka fito ba."