Duk Aka Zaɓi Ahmad Aliyu Zaman Lafiya Zai Samu a Gabascin Sakkwato----Ibrahim Lamido

Duk Aka Zaɓi Ahmad Aliyu Zaman Lafiya Zai Samu a Gabascin Sakkwato----Ibrahim Lamido

 

Dan takarar Sanata a jam'iyar APC yankin Sakkwato ta gabas Honarabul Ibrahim Lamido ya baiwa mutanen gabascin Sakkwato tabbacin za a samu tsaro, aminci ya dawo a yakin matukar suka zabi dan takarar gwamna a jam'iyar APC Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto.

Ibrahim Lamido a kalamansa da ya gudanar a kananan  hukumomin Isa da Sabon Birni lokacin yekuwar zaben da jam'iyarsa ta gudanar a satin nan  ya ce irin yanda jam'iyarsu ta damu da harkar tsaron gabascin Sakkwato yana da tabbacin Ahmad Aliyu zai yi komai domin ganin ya magance matsalar tsaron da ake fama da shi sabanin wannan gwamnati da ke yi wa hrkar tsaro rikon sakainar kashi.
Lamido ya kalubalanci mutanen PDP da suke raya son mutanen Isa da Sabon Birni amma suka kasa zuwa yi masu jaje a duk sanda lamarin rashin jin dadi ya same su balle su bayar da tallafi gare su, kan haka ya nemi masu kishi da ka da su baiwa jam'iyaar PDP kuri'unsu don ciyar da yankinsu gaba.
Ibrahim Lamido ya kara tabbatar da matukar ya samu nasarar wakiltar yankin Sakkwato ta Gabas za su samu wakilci nagari da zai saurari koken jama'a da nufin magance matsalarsu.
Ya ce zai hada kai da gwamnatin tarayya da jiha domin kawaowa yankin abubuwan cigaba a haujin ilmi da kiyon lafiya da sauran abubuwan more rayuwa.