DUHU DA HASKE: Fita Ta 29

  DUHU DA HASKE: Fita Ta 29


  


     Na
*Jiddah S mapi*


*Chapter 29*


                 ~Manal cikin wani irin murya tace "momy...?"
da ihu tace "shiru, karki fara wannan kuskuren na kirana da mamanki ni ban haifi annoba ba, dama a cikin hauka na haifeki ban ma san na haifeki ba, kuma ba zansa a raina na haifeki ba, tun kamin na ganki na jima da kwashe miki albarka, na tsaneki na tsani halinki, mutanen da suka taimaka miki suka ɗaukoki daga bola su kika sakawa da sharri, keba ƴata bace ke ƴar bola ce, ba nice na haifeki ba shaiɗan ne ya haifeki akan bola"
wani irin kallo manal take mata, badan an rufeta a inda take ba da babu abinda zai hanata kashe wannan matar da akace uwarta ce anan idan yaso a haɗa duka laifukan ayi mata hukunci, kuka momy take yi sosai, abba ne yazo ya rike hanunta ya jata zuwa wajen zamanshi ta zauna tana cigaba da kuka, alkali yayi shiru bayan ya gama sauraran komai, kotu duk akayi shiru babu me magana sai saurin kukan momy, Ammi tazo gaban alkali ta mika memory tace "nayi recording duk abinda ya faru a ranan da Imran yazo harma da sauran ranakun da take yin abinda babu kyau akwai videos"
alkali ya karɓa yace a kunna babban tv sannan asa memory, kunnawa akayi akasa memory muryan manal sukaji lokacin da Imran ya shigo har zuwa lokacin data tureta akan stair, sannan ta bada video ɗin lokacin data kona dady da kuka sauran videos ɗin, shiru akayi manal kanta a kasa, abdool yana daga tsaye saida ya zauna dan rashin lafiya sosai yake ji, Alkali bayan an gama sauraran yace "duba da irin laifukan da manal ta aikata masu girma, kotu ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyan rataya, kafinnan zatayi zaman prison na sati ɗaya sannan rana ita yau wato ranan talata kowa zai hallara a kotu domin yanke mata hukunci"
daga nan aka tashi a kotu, manal kanta a kasa babu wanda ya isa yace ga halin da take ciki, police ne yazo zaisa mata ankwa, kanta kasa da kakkausan murya tace "babu dokan da yace namiji ya kama mace inaga zaifi kyau ku turo mata su samin"
mata aka samu suka sa mata ankwa sannan suka riketa, fitar da ita akayi daga wajen daidai zasu wuce ameesha wacce take kusa da ammi manal ta tsaya ta kallesu su duka, murmushin gefen baki tayi tace "kuna ganin kunyi nasara akaina? kuna ganin zan barku kuji daɗin rayuwarku ne? ai tunda kuka yadda manal ta shiga rayuwarku tofa babu me cetonku"
kallon abdool tayi sannan tace "Allah ne ya samin son abdool a raina, wallahi ba zan taɓa barinshi ba koda na mutu, sannan babu ku babu farin ciki, duk family ɗinku ba zan bari ku samu farin ciki ba saina ɓata komai....."
maruka masu zafi abdool ya wanketa dasu, zatayi magana ya kara ɗauketa da mari, da mamakinsu sukaga an fara janta tana tafiya tana magana "wallahi ko kasheni zakuyi ba zan barku ba, saina ɓata komai"
fita akayi da ita, sai a lokacin abdool ya silale kasa zai faɗi ameesha ce tayi saurin rikeshi, cikin azaban yunwa da rashin lafiyan da yake ciki ya faɗo jikinta, saide yafi karfinta saida ya faɗi kasa, ammi tayi saurin rikeshi, yazeed dake zaune yayi shiru Abba yace "jeka taimaka mishi mu kaishi gida hanan ta dubashi"
tashi yayi yaje inda suke ɗaukanshi sukayi suka fita dashi zuwa mota, duk suka shiga motar banda ammi da baba, a motar ammi suka shiga ammi da kanta ta jasu suka bi bayansu, koda suka isa gida a extra ɗaki aka kwantar da Abdool Imran da fahad ne suka samo ruwa me ɗan zafi suna goge mishi jikinshi da towel, hanan kuma ta fita zuwa neman allurai da magani, yana kwance akan gado idonshi rufe ameesha suna tsaye a kanshi duk hankalinsu a tashe, hanan ce tayi sallama ta shigo da leda a hanu, fara fixing drip tayi tace "rashin cin abinci da cizon sauro da kuma ɓacin rai da yawan tunani yasa mishi wannan mummunan ciwon, a gaskiya ya hawala sosai, daya kara kwana ɗaya a haka gaskiya zai iya mutuwa"
shiru ameesha tayi, ruwan ya fara tafiya a hankali sannan tayi mishi Alluran a cikin ruwan, duk sun kasa tafiya suna tsaye harda momy dake aikin kuka, cikin kuka tace "kenan nice na haifi ƴar data jefa kowa cikin damuwa?"
kuka take yi sosai Abba ne ya fita da ita dan lallaɓata, Imran ya zauna a kasa dirshan ya jingina kashi da jikin gadon, fahad kuma ya zauna a gefe yayi tagumi, yazeed da hanan suna wajen suma cikin tausayawa halin da suke ciki, yazeed yace "ku daure insha Allah zai samu sauki"
Ameesha zama tayi a bakin gadon idonta yana cika da zafafan hawaye, a hankali ta kwantar da kanta akan pillow da kanshi yake, tayi shiru fuskanta kusa da nashi tana kallon yadda kaykkyawan fuskanshi ya cika da gashi, hawaye masu zafi suka fara zubowa ta kasa sharewa sai kallonshi take, ammi ta shigo tareda baba, zama sukayi ammi a kusa da ameesha kan gadon baba kuma ya zauna akan sofa yayi tagumi, ammi kallon ameesha take wacce take kallon Abdool tana hawaye, a hankali ta rike hanunshi da babu drip ta damke ta runtse ido hawaye suna cigaba da zuba.

bai farka ba har an fara kiraye kirayen sallan mangrib, a hankali ameesha ta tashi cikin muryanta da baya fita tace "muje muyi salla"
kowa ya mike a sanyaye zasu je salla, ji tayi ya rike hanunta cikin dashashen murya yace "meesha"
kasa juyowa tayi sai hawayen dake zuba, yayi yunkurin tashi yace "meesha"
bata juyo ba kuma bata zame hanunta ba, yazeed dake bakin kofa ya dawo a hankali ya cire hanun Abdool a cikin na ameesha sannan ya taimakawa abdool ɗin ya tashi a hankali yana ciza baki, kallon ammi yayi yace "ammi dama kina magana?"
murmushi tayi tace "yau ba ka gani ba Abdool?"
yace "meyasa kika ɓoye?"
tace "sabida ina jiran ranan daya dace kafin na bayyana kuma yau ne ya dace"
shiru yayi ya kalli bayan ameesha wacce taki ta juyo, kawai yace "baba a bani tea ina jin yunwa"
hanan tayi saurin cewa "bara naje na kawo maka Imran muje"
tayi maganan tana jan hanun Imran wanda yake shirin fara kuka ganin halin da yayanshi yake ciki, babu jimawa suka shigo da tea ammi ce ta bashi, yana gama sha yace "abinci"
abinci hanan ta kawo mishi yaci sosai kafin yace "zanyi salla"
yazeed ne ya rikeshi ya kaishi toilet sannan ya fita, saida yayi wanka da ruwan zafin da yazeed ya haɗa mishi, saida ya gama yace "na gama"
shiga yazeed yayi ya fito dashi daga toilet ɗin ya shimfiɗa mishi sallaya time ɗin duk sun fita yin salla ya rage su kaɗai, jallabiya ya ɗauko mishi sabo dal, karɓa yayi zaisa sai kuma ya rufe ido yace "i can't"
yazeed ya kula baison ciwo wannan ko kaɗan, karɓa yayi ya cire mishi towel ɗin sannan yasa mishi jallabiyan, a zaune yayi sallan, yazeed ya taimaka mishi ya koma kan gadon ya kwanta, zai fita yaji man yace "bro?"
a hankali ya juyo sai yaji jikinshi yayi sanyi, bai taɓa jin wannan kalman na bro ya daki zuciyanshi ba kamar yadda yaji yanzu, sai yaji kamar ɗan uwanshi ne na jini ya kirashi da sunan, yace "na'am akwai abinda kakeso ne?"
gyaɗa kai yayi, ganin yayi shiru, yazeed ya dawo ya zauna kusa dashi yace "me kake so?"
yace "ameesha nakeso ka tayani bata hakuri da nemamin gafara a wajenta nasan nayi laifi, i want my old friend"
shiru yayi yana kallonshi, sai kuma yace "okay ba komai karka damu"
yace "thank you"
fita yayi yaje yayi salla, ameesha tunda tayi salla take zaune akan sallayan bata da niyan tashi, hanan data idar tace "bari naje na kara duba patient ɗina"
batayi magana ba har hanan ta fita, koda taje tace "sannu da jiki"
yace "yawwa sannu kema"
tace "me yake maka ciwo yanzu?"
yace "babu"
tace "good Allah ya kara lafiya amma ga wannan maganin kasha zai saka bacci sosai idan ka tashi zaka ji normal jikin zai kara sauki"
karɓa yayi ta bashi ruwa yasha, yace "na gode"
fita tayi ta samu momy a falo ta gaji da kuka harta gode Allah, idanunta sun kumbura, zama tayi a gefenta ganin tayi tagumi tace "momy me haka?"
hanunta ta rike tace "hanan ban samu haihuwa ba tsawon shekaru kullum ina addu'a Allah ya bani haihuwa, yau naga ƴar dana haifa amma naji na tsaneta, sai naji na tsani haihuwan ma gaba ɗaya"
rungumeta hanan tayi tasan ba zata iya hanata kuka ba sabida ɗa ya wuce wasa.

Zaune take tayi shiru a cikin prison ɗin kanta jikin bango tana kallon kofan da aka rufeta, a hankali take ɗan bubbuga bayan kanta a jikin bangon, uniform na prisoners ne a jikinta ko ɗankwali basu bata ba
"ni ban haifi annoba ba, shaiɗaniya ce ta haifeki akan bola, daga bola muka tsinceki, yarinyar data kashe wanda ya riketa, sannan ta ture wacce ta ɗaukota daga bola akan stair, na tsaneki manal bana sanki"
toshe kunnuwa tayi tace "no manal no"
hawaye masu zafi suna bin kuncinta, wata mata ce me kula da prisoners mata ta shigo ta tsaya a bakin kofa tana kallon manal, karasowa ciki tayi tace "ba zama ya kawoki nan ba tashi kije kiyi aiki, akwai faskare sannan akwai wanki maza tashi"
shiru tayi bata kulata ba, cikin tsawa tace "baki jini bane?"
ko kallonta batayi ba, matar tace "okay taurin kan naki zaki gwadamin anan ma kenan to shikenan mun kulla dani dake"
gashinta ta kama da karfi ta fara janta, cikin jin zafi tace "ki sakemin kaina"
janta take a kasa by fire by force, mutane suna kallonsu har ta kaita can inda sauran suke aiki, wurgata tayi akan tulin wankin da yafi na kowa sannan ta wurga mata omo tace "na baki 20mins idan baki gama ba zan kara miki wani"
tafiya tayi ta barta a wajen, kanta kasa idanunta sunyi jajur tana kallon wankin da yake da uban datti, a hankali ta tashi ta daure baya da gaban rigan ta ɗau bahon dake wajen ta tafa tafiya zuwa inda taga mata suna ɗiba ruwa, aje bahon tayi a layi tana jira kowa ya gama ɗibawa kafin ta ɗibi nata, tana tsaye a wajen har akazo kanta zata sa taga wata mata tazo tasa nata a ciki kuma yanzu tazo, batayi magana ba har matan ta cika bahonta taf da ruwa, kallon manal tayi wacce ta ɗau nata zata sa, rike bahon matar tayi tace "ban gama ba sai nasa ɗayan da za'a kawo min yanzu"
manal tace "sake"
matar tace "ba zan sake ba"
ta kuma cewa "sake"
tace "ba zan sake ba"
kanta ta rike ta tsoma cikin ruwan data cika, numfashi ta fara ja a wahale tana kwace kanta, ko gezau manal batayi ba ta danna kan cikin ruwan, matan dake wajen duk suka zaro ido a tsorace sukayi baya suna ganin ƴar uwarsu tana magagin mutuwa, hannu take ɗagawa tana neman taimako, da gudu wata a cikinsu taje ciki tana haƙi ta zube gaban masu kula dasu tana nuna wajen ta kasa magana, ɗaya a cikinsu yace "menene?"
da kyar tace "za'ayi kisa, wannan sabuwar prisoner ɗin tana can zata kashe rukayya"
tare suka fita a guje, har zuwa lokacin kan matar yana cikin ruwa, dukansu suka haɗu suka janyeta, faɗuwa tayi kasa kamar batada rai, matar dake kula dasu tasa hannu a cikinta da karfi tana dannawa, da kyar ta fara fitar da ruwan idanunta a sama, hamdala sukayi ganin tanada rai, tasa a ɗaure mata manal, sanda mafi kauri da girma ta ɗauka ta fara dukan manal kamar itace ta haifeta, saida ta gaji dan kanta sannan tasa a kwance ta, wurgar da ita tayi akan kayan tace "wanke kuma kin shiga time ɗinki"
cikin azaba ta fara wankin, tana layi da kyar ta gama tulin wankin ta gaji likis har wani jiri jiri takeji, tafiya zatayi ta kwanta matar tazo ta tsaya a gabanta tace "manal umar maidawa, Au manal ƴar mahaukaciya kin gama wanki saura faskare"
shiru tayi, ta rike hanunta tana janta har zuwa wajen faskaren ta wurgata tace "maza fara"
ɗaukan gatari tayi ta fara faskare tana rufe ido, faɗuwa tayi kasa tana sauke numfashi, da kyar taja jiki ta tashi tana cigaba da faskaren saida ta kasa ɗaga koda yatsa ɗaya kafin matar tazo ta kara janta zuwa cikin ɗakinta ta wurgata ta rufe da key, numfashi take yi da kyar.

Abdool jikinshi yana sauki hanan ta dage mishi da magani yazeed dasu Imran suna kula dashi sosai, saide har yanzu baiga ameesha ba, bata shigowa kuma bai tambayi kowa ba, yana zaune a ɗakin da Abba ya basu a gidan yayi shiru yana kallon hotonsu wanda suka ɗauka family lokacin dasu umma suke raye, hawaye yake yi cikin kuka yace "komai ya ɓaci, ameesha ma ta daina kulani, kullum cikin ciwon zuciya nake, Anty da umma kun tafi, ameesha ma bata kulani ta daina sona"
yazeed dake tsaye a bakin kofa yayi shiru yana kallonshi, jiki a sanyaye yayi gyaran murya da sauri ya ɓoye hoton yace "bro kaine?"
shigowa yayi ya zauna, yana sanye da jallabiya maroon yayi kyau sosai, abdool yace "baka fita bane yau?"
yace "ban fita ba ina gida"
yace "okay"
kallanshi yake yana jin tausayinshi, yace "zaka yadda mu fara aiki tare?"
shiru abdool yayi, yace "zaka yadda?"
a hankali yace "aikin me?"
yazeed yace "company Abba ya buɗe mana a Abuja jiya na fashion designing tunda ka kware a zane zamu koma can da zama inji Abba bayan sati ɗaya, sabida yace zama anan ba zaiyi ba, kuma har sunyi magana da baba da kuma ammi, da sunanka Abba ya buɗe company sabida a yanzu kaine zaka rinƙa kula dasu Imran da kuma su baba, hakan zai faru ne idan ka manta komai da komai daya faru a baya"
takadda ta ciro daga aljihu ya mika mishi yace "wannan shine company sannan sun bani ne na baka da kaina a matsayin ƴan uwan juna"
yayi shiru yana kallon yazeed, ganin bai karɓa ba ya rike hanunshi ya damƙa mishi yace "come on be a man ka daina wani langwaɓewa kamar mace, sabida kaga kanada kyau fuskanka kamar na mata shiyasa kake wannan shagwaɓan? mutane suna cewa na fiye shagwaɓa amma tunda na ganka na baka award a shagwaɓa, rashin lafiya kuka, farin ciki kuka, damuwa kuka, tuna baya kuka, rashin ganin ameesha kuka, komai sai kayi mishi kuka?"
shiru yayi, yace "please ka rage wannan shagwaɓan kaji?"
a hankali yayi murmushi, yace "ko kaifa, kaga zamu koma abuja bayan an yankewa wannan manal ɗin hukunci idan mun tafi mun manta da komai zamu fara sabon rayuwa"
a hankali yace "to"
ganin yana hawaye ya amsa yace "amsawa ma kuka?"
dariya yayi, ammi ce ta shigo tayi kyau cikin baƙin hijab, hanunta rike da cup ta zauna kusa dasu tace "maza buɗe baki"
shiru yayi yana kallonta a shagwaɓe yace "ammi nayi sauki"
tace "sha nace"
karɓa yayi kamar zaiyi kuka ya shanye, tace "saura kwana uku shiga kotu, daga nan zamu wuce abuja, babanka yace na sanar maka domin yau yaje yola akwai saƙon da yakeso ya ɗauko"
yace "to"
zata tafi taga ya bita da ido da alama akwai tambayan da yakeso yayi mata, murmushi tayi tace "ameesha tana lafiya ta tafi aiki ne"
a hankali ya sunkuyar da kai, yace "ammi zan fita yanzu amma zan dawo bada jimawa ba"
ammi tace "ban yadda ba saide ku fita tareda yazeed duk inda zaka je"
yace "to"

kallon yazeed yayi yace "zaka rakani?"
yace "why not?"
tashi yayi yace "muje idan a shirye kake"
ganin shima jallabiya ne a jikinshi me kyau a jikinshi suka fita, a motar yazeed suka fita daga gidan, yazeed yace "ina zamuje?"
yace "prison"
kallonshi yayi da matukar mamaki sai kuma yayi shiru ganin ya ɗauke kai yana kallon titi.

manal cikin sabo da wahalan take ɗibo ruwa tana kaiwa randa, duk matan babu wacce take yadda ta shiga harkanta tun abinda ta yiwa rukayya, tayi baka sosai ta lalace musamman gashinta daya ɓaci sosai, a galabaice take tana rike da roban ruwa kamar zata faɗi, sam batada karfi ko kaɗan, matar tazo tace "ke aje roban ruwan kizo kinyi baƙi"
shiru tayi jin tayi baƙi tasan batada wani wanda zasu zo a halin yanzu, 
"ba magana ake miki ba?"
aje roban ruwan tayi cikin azaban wahala ta fara jan kafanta da yake ciwo ta bi bayanta, tun daga nesa ta ganshi ya jingina da jikin kofa yayi shiru yana kallonta tana karasowa, murmushi tayi mishi wanda rabon da tayi irinshi tun kafin a kawota wannan wajen me cike da azaba, tace "my abdool"
zata rungumeshi ya matsa ta faɗa akan kofan, hanu ya zuba a aljihu yana kallonta yace "manal yau shine rana ta karshe da zan samu daman magana dake, daga nan saide a lahira idan zamu haɗu dan inada tabbacin ba zanbi ta layin da kike ba ma'ana layin ƴan wuta, nazo ne na baki wani kyauta amma kada ki karanta saina bar nan"
hanunta ya rike ya damƙa mata wani farin takadda yace "na gode da komai, na gode da jefa rayuwata da kikayi cikin masifa, na gode da kashe Anty da sanadin mutuwan umma, sannan na gode da sharrin da kika yiwa kanina sannan kikamin nima, na gode da rabani da wacce muka taso tare na gode da komai da komai" daga nan ya juya
tafiya yayi, tana tsaye tana kallonshi har ya tafi, buɗe takaddan tayi taga ya rubuta "ni Abdulrahman haruna lamiɗo na saki matata manal umar maidawa saki ɗaya"
murmushi tayi sannan tace "koba komai zan kwana yau cikin farin ciki, naga abdool sannan yamin saki ɗaya ba saki uku ba, hakan ya nuna har yanzu yana sona a ranshi, abdool kaima ba yin kanka bane soyayya gaskiya ce, duk yadda zaka danne ba zai taɓa dannuwa ba"
Abdool a hanyan komawa yace "kayi mamakin zuwana wajen manal ko?"
shiru yayi dan gaskiya yayi mamaki, abdool tace "takaddan saki na kawo mata na saketa"
murmushi yayi a fili yace "Alhmdllh".

Judah Ce..