DUBARU DA SINADARAN HADA MIYAR WAKE TA ZAMANI

DUBARU DA SINADARAN HADA MIYAR WAKE TA ZAMANI
ZEZA'S CUISINE
 
MIYAR WAKE 
 
Abubuwan hadawa
 
Wake
Manja
Attarugu
Bushenshen kifi (banda)
Albasa
Maggi
Kori
Cittah       
Tafarnuwa
Gishiri
Yadda ake hadawa
 
Da farko dai zaki wanke wakenki ya fita sosai
Sai ki dora ruwan ki a wuta ya tafasa, sai ki zuba wakenki ya yi ta dahuwa har sai ya nuna ya yi lukwui
Sai ki zuba jajjagaggen attarugu, da albasa, da manja, da kifinki, sai ki jira miyanki har sai ya tatafasa. Za ki ji yana kamshi
Sai ki zuba maggi, da kori, da cittah, da tafarnuwa, da gishiri, sai ki barshi kamar minti sha biyar za ki ji gida ya dau kamshi
Da zarar kin duba miyarki tayi shikenan sai ki sauke
Zaki iya cin miyanki da tuwon shinkafa .
(Zainab Muhammad jibril)
Zeza's cuisine
 
Enjoy
 
Share✅
Edit❌