Ƙungiyar mata musulmi ta Nijeriya reshen Sakkwato(FOMWAN) ta yi shiga sahun masu murna kan ranar yara mata ta Duniya a 2026, in da ta mayar da hankali kan ilmin mata da tarbiyarsu da kiyon lafiyarsu a mahangar daular Usmaniyya.
Farfesa Sa’adiya Omar tsohuwar Amira ta ƙasa kuma ɗaya daga cikin mambobin kwamitin amintattu na ƙungiyar ta bayyana cewa sun gudanar da taron ranar ‘ya’ya mata ne saboda ware ranar da majalisar ɗunkin duniya ta yi domin zaburar da mata a fannoni daban daban.
“A kowace shekara duniya ta tsara 11 ga Okotoba ta zama ranar ‘ya’ya mata akan a dubi jigon rayuwa da yakamata a tattauna kansa, in da wannan shekara za a yi magana kan ilmi da tarbiya da sauransu.
“A matsayinmu na ƙungiyar addinin musulunci duk abin da aka kawo mana sai mun duba shi ta mahangar addinin musulunci kan haka muka yi wa jigon kwaskwarima don ya dace da addini da al’adarmu.
“Mun tsara gabatar da ƙasidu kan yadda jihadin ɗanfodiyo ya kula da ilmin mata, da gabatar da tarihi kan Nana Asma’u ‘yar Mujaddadi Shehu Usman Fodiyyo, yadda ta koyar da mata ilmi da sana’a, da tattauna ƙalubalen da ake samu a tsakanin mata da yanda za a magance su a cikin al’umma.
“Mun duba yanda mace za ta kula da jikinta bisa karantarwa addini, ta kuma kaucewa sabuwar yaudara da aka fito da ita cewa ‘mace ita ke da jikinta’ don haka tana iya yin komai ta ga dama, wannan komai ɗin matsala ce domin har zina tana iya yi ba wanda ya isa ya hana ta, addinin musulnci bai aminta da wannan ba, al’umma da iyaye da Allah wanda ya halicce ta suna da haƙƙi kan ‘ya mace kowa akwai buƙatar kiyaye dokokinsa a matsayinmu na ƙungiyar addinin musulunci mun shirya wannan taron domin ilmanatar da ‘ya mace musamman waɗanda suka zo daga makarantu, muna fatan wannan ilmantarwa ya amfane su da al’umma baki ɗaya.”
Dakta Ibrahim Liman Sifawa ya gabatar da ƙasida kan ilmin ‘ya’ya mata, a wurin ya jawo hankali kan yadda rashawa ta yi tasiri a cikin jama’a wanda hakan ya ƙara yawan jahilci kuma mata ne suka fi cutawa da rashin adalcin da ake yi.
“Hakan ya sa ɗanfodiyo bai yi wasa ga baiwa mata ilmi ba, domin suma mutane ne, duk aka samu zalinci da jahilci suka yawaita mata sun fi jin jiki ba a kula da haƙƙoƙinsu, kowa akwai abin da aka ɗaura masa na wajibi tsakanin mata da maza dole ne a karanatar da kowa da baiwa mata kulawar da ta dace da su. Babban jihadi ne ka faɗawa shugaba abin da ake yi ba daidai ba domin a gyara.”






