Dokar Zabe:Akwai yiwuwar Tafiya Kotu---Malami

Dokar Zabe:Akwai yiwuwar Tafiya Kotu---Malami

 

Ministan shari'ar Nijeriya Abubakar Malami bayan kammala zaman majalisar zartawar gwamnatin Tarayya a Laraba ya ce gwamnati nada zabi guda uku kan dokar zabe da aka sanyawa hannu wadda majalisa taki amincewa ta sake yiwa gyara. 

Ya ce zabin da gwamnati take da shi ko ta nemi a sake duba dokar, ko ta garzaya kotu, ko kuma ta karbi dokar yanda take.
Ya ce a duk lokacin da majalisar dokoki ta kasa ta yi aikinta gwamnati nada damar aiki da nata dama kan abin da majalisa ta zartar.
Ya ce har yanzu gwamnati ba ta yi matsaya kan abin da za ta yi ba kan lamarin har yanzu gwamnati na duba abin da za ta yi kan kin sake gyaran fuska da majalisar dattijai ta yi kan lamarin bayan shugaban kasa ya aika mata kudirinsa nason sake gyaran fuka ga sashe na 84(12).