Dillalan Man Fetur A Fadin Najeriya Sun Tsunduma Yajin Aiki

Dillalan Man Fetur A Fadin Najeriya Sun Tsunduma Yajin Aiki

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta umarci mambobinta a fadin kasar nan da su tsunduma yajin aiki daga yanzu har sai abin da hali ya yi, dukkansu su rufe gidajen man su da suke sayarwa.

Shugaban kungiyar IPMAN, Mohammed Kuluwu, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ranar Talata a Maiduguri. 

Hakazalika Mohammed Kuluwu ya umurci mambobinsa su daina siyan mai daga wajen depot sai lokacin da hali yayi. 

"Halin da muke ciki kan  saya da sayar da mai, an  wajabtawa mambobinmu sayar da mai a farashin da faduwa zamu yi."  Ya ce Kungiyar za ta ci gaba da tuntuba, kuma za ta sanarwa mutane abin da ake ciki a lokacin da ya dace.