DAY 3: @RamadanKareem: Yadda Za Ki Yi GASASHIYAR KAZA Don Faranta Rayuwar Iyali
BASAKKWACE'Z KITCHEN
DAY 3: Ramadan Kareem
GASASHIYAR KAZA
INGREDIENTS
Kaza
Man gyaɗa
Barkono
Kayan kanshi
Magi
Tafarnuwa
Gishiri
Kori
Ganyen fasili
Albasa
Lemun tsami
METHOD
Aunty na idan kika samu kazar ki sai ki wanke. Daga nan sai ki sata a tukunya ki zuba mata mangyaɗa ki kawo kayan ƙamshi ki ki shafe jikin ta da shi sai ki kawo jajjagaggiyar tafarnuwa ki Sannan ki kawo barkono da garin kori, sai ki cuccuɗa ki shafe naman kazar nan ko ina na nama ya cuɗanya da kayan haɗin nan na ɗanɗano.
Daga nan sai ki ajiye kamar awa biyar ko kuma ki yi haɗin tun dare ya shiga jikin naman sosai.
Daga nan ki tura lemun tsamin ki a cikin naman kazar nan ki ajiye a gefe. Sai ki ɗauko farantin gashi ki ɗaura dunƙulen kazar ki sannan ki ɗauko ganyan fasili ki zuzzuba a kai don kwalliya. Sai ki sanya shi a cikin Oven ki bar shi ya gasu zuwa 30munites. Idan ya gasu zaki ji ƙamshi na tashi sai ki fito da shi ku ci.
Iyalanki za su baki labarin yanda suka ji da wannan haɗin na musamman da kika yi masu.
MRS BASAKKWACE
managarciya