BASAKKWACE’Z KITCHEN
DAY 15 @RamadanKareem: Yadda Za Ki Hada MEAT ROLL Mai Dadin Gaske
INGREDIENTS
fulawa
meat
tarugu
albasa
maggi
kayan ƙamshi
karas
kabeji
lawashi
METHOD
Da farko zaki kwaɓa fulawar ki kwaɓin meat pie,se ki ɗauko dafaffiyar nikakkiyar naman ki na rago ko na san ki da kika riga rika kika dafa ta da kayan ƙamshi ,,se ki ɗauko kayan miya da kayan kamshin ki da karas ki zuba a kasko,da dan mangyada kadan,se ki sauke ki zuba kabejin ki jujjuya,tiriri ze dafar da kabejin ,se ki tsakuda shi waje ɗaya,kita juyawa ya soyu sama sama,se ki dauko fulawan ki aunty na ki murza ta ta fale fale ,ki samu reza ki yanka shi a tsaye se ki debo hadin nikakkiyar naman ki, ki zuba ki nannade kamar tabar ma,nadewar fa sosai zakiyi gudun karya watse a cikin mai,se ki sa a cikin mangyada ki soya ye ja se ki kwashe shikenan.
MRS BASAKKWACE





