Dangantaka Tsakanin Masarautar Sarkin Musulmi da Gwamnatin Sokoto Ta Yi Tsami

Dangantaka Tsakanin Masarautar Sarkin Musulmi da Gwamnatin Sokoto Ta Yi Tsami

Gwamnatin Sakkwato karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu tun bayan shigowar ta saman mulkin jihar a satin farko ta bayar da sanarwar dakatar da wasu uwayen kasa da tsohon Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya aminta da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar ya nada kwanaki kadan kafin barin Gidan gwamnati.

Dakatar da sarakunan ya Sanya mutane da dama suka jefa ayar tambaya kan dangantakar masarauta da gwamnatin jiha. 

Jama'ar jihar Sakkwato Sun fahimci akwai tsamin dangantaka a bangarorin biyu a lokacin bukin sallah babba(layya) in da Gwamnan Sakkwato ya ki Kai gaisuwar sallah a fadar Sarkin Musulmi, wannan dadaddiyar al'ada ce da aka Saba da ita a tsakanin shugabanni, hakan ya sa da yawan mutane suka dauka abubuwa ba su tafiya daidai.

Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shattima ya kawowa Sarkin Musulmi gaisuwar sallah ya nemi  Gwamna ya mutunta sarkin musulmi domin shi jagora ne a Nijeriya.

Ya ce Sarkin Musulmi shugaban ne ba a Arewa ko Nijeriya ba a Afirika gaba daya.

Bayan wucewarsa aka fahimci abubuwa sun sauya an yayyafawa lamarin ruwa.

A wannan satin tsamin dangantaka ya sake kunno kai in da sarakuna 10 da ‘yan majaisar sarkin musulmi biyar da suka hada da Sarkin Kabin Yabo da Sa'in Kilgori da Sarkin Yakin Binji da Sarkin Gobir da kuma Baraden Wamakko,  ke dakon matakin da gwamnatin Sakkwato za ta dauka nan gaba sakamakon kwamitin da gwamnatin ta kafa musu kan zargin aikata laifuka masu alaka da siyasa.

Sarakuna iyayen al’umma ne  suna ba da gagarumar gudunmuwa don daidaita lamurra sai dai wasu lokutta sukan fada tsaka mai wuya in an zarge su da tsoma baki a lamurran siyasa in da yake kai ga rasa kujerarsu ko a rage masu girma.

A Sakkwato 'yan majalisar Sarkin Musulmi da uwayen kasar na jiran matakin da gwamnati za ta dauka bayan an gurfanar da su a gaban wani kwamiti da gwamnati ta kafa kan zargin sun taka rawar ganin jam’iyar PDP ta samu nasara a zaben da ya gabata na 2023.

Wata majiyar ta kusa da sarakunan ta tabbatar da an gayyaci sarakunan a Laraba kuma sun bayyana gaban kwamiti a ranar Alhamis  data gabata, an karanta musu korafe-korafen da mutanensu suka yi kansu, an nemi da su kare kansu kuma hakan suka yi.  

Sarakunan  sun ki aminta su yi magana da manema labarai kan lamarin.

Sakataren yada labarai na jam’iyar PDP a Sakkwato Hassan Sahabi Sanyinnawal ya ce a gefen su sarakuna iyayen al’umma ne ba ‘yan siyasa ba “ba za mu yi mamaki ba in an kira su ne domin a ci mutuncinsu ko musguna masu kowa ya sani a Sakkwato tarihi ne zai maimaita kansa a lokacin tsohuwar gwamnatin da Tambuwal ya gada(Gwamnatin Sanata Wamakko), kai ka sani al’umma sun sani akwai sarakuna da yawa da aka ci mutuncinsu wasu aka raba su da kujerunsu wasu aka sauya musu wurin aiki, kasa da in da suke.

“Mu a jam’iyar PDP ba mu tunanin akwai wani sarki da ya yi jam’iyar APC ko PDP sabanin su da suke tunanin hakan”, a cewar Hassan.

Kwamishinan yada labarai na jihar Sakkwato wanda kuma shi ne sakataren yada labarai na APC a jihar Alhaji Sambo Bello ya tabbatar da gayyatar ya ce gwamnatinsu mai adalci ce kuma za ta yi adalci ga kowa, “na farko dai kwamiti ne ba jam’iya ba shugaban jam’iyar APC a jiha Alhaji Isah Sadik Acida  mamba ne a kwamitin akwai sarakuna da ma’aikatan gwamnati a ciki, maganar musgunawa wasu sarakuna zargi ne kawai ba gaskiya ba ne.

“A jira kwamiti ya kammala aikinsa, ba shakka zai yi adalci".

Jami'in hulda da jama'a na fadar sarkin Musulmi ya ce ba su da masaniya abin da ake ciki na kwamitin.

Masu sharhi kan lamurran yau da kullum a Sakkwato suna ganin wannan kwamitin da gwamnatin Sakkwato ta samar kuskure ne da zai iya kawo mata cikas a harkokin gwamnati a gaba domin sarakuna suna goyon bayan gwamnati ne a kadayaushe, in sun hukunta wadanda suka goyi bayan tsohuwar gwamnati su ma bayan sun tafi za a hukunta wadanda suka goyi bayan su.

Suna ganin da matsala a kwamitin tun da aka boyewa al'umma sanin su waye mambobin kwamiti da shugaban, har wadanda suka je gaban kwamitin ba su San wane ne shugaba mai cikakken iko ba.

Domin sanin shugaba da mambobin kwamiti da manufar kafa kwamitin duk kokarin jin ta bakin Mai magana da yawun Gwamna Abubakar Bawa ya ci tura.

Alhaji Yusuf Dingyadi a turakarsa ta Facebook ya ba da shawara kan lamarin ya ce "duk wani mataki da gwamnatin jahar Sokoto zata dauka akan uwayen kasa na zargin yin siyasa ko shiga lamuran siyasa, hakika rashin adalci ne da cin zarafi; don kuwa akwai daga cikin uwayen kasa da suka goyi bayan zuwan gwamnatin dake kan mulki a yanzu, su kuma fa?

"Idan har 'yan adawa sun kasa tsamo su daga wannan bita-da-kulli da ake kitsawa, ta tabbata al'umma jahar Sokoto da lokaci za su kasance alkalai kan wannan matakin na gwamnat.

"Don haka, Mai girma Gwamna jahar Sokoto, Dakta Ahmed Aliyu Sokoto ya yiwa Allah ya hana wannan cin zarafin da yanzu haka ya jefa al'ummarmu cikin tunani da ganin rashin kyautatawa.

"Mai girma Gwamna ya tuna da ya rantse da Allah yana rike da Alkur'ani mai tsarki cewar, ba zai ci zarafi ko fiffita wani akan wani ko barin hakan ta faru akan kowane dan jahar Sokoto, a bisa alkawali wanda Allah (SWT) da Mala'iku da jama'a duk sun shaida akan haka lokacin rantsuwarsa.

"Allah Ya taimaki Gwamna ya bashi ikon kiyaye rantsuwarsa bisa gaskiya da adalci", kalaman Dingyadi.