Dan majalisa ya nemi agajin Gwamnatin Sakkwato bayan ambaliya ta mamaye kauyukka 6 

Dan majalisa ya nemi agajin Gwamnatin Sakkwato bayan ambaliya ta mamaye kauyukka 6 
 
Dan majalisar dokokin jiha da ke wakiltar karamar hukumar Sabon birni ta kudu Aminu Mustafa Boza ya nemi majalisa ta yi kira ga gwamnatin Sakkwato da hukumomin da ke kula da ruwa a gwamnatin tarayya da hukumar na da agajin gaggawa su katse  ruwa zuwa kauyukkan da ambaliya ta shafa a gefensa.
"Kauyukkan su ne Makuwana, Dangawo, Faru, Gumbula, 'Yan Faruna da  Magajin Dawaki, haka kuma bayan ambaliyar ta mamaye su ta kwashe hanyar da ta hada Karamar hukumar Goronyo da Sabon Birni."
Boza a zaman majalisa wanda mataimakin shugaban majalisar Alhaji Kabiru Ibrahim ya jagoranta ya nemi majalisa ta jawo hankalin hukumomi kan ambaliya da ta mamaye kauyukkan, hadi da babbar hanyar karamar hukumar Sabon Birni da ruwan suka kwashe.
Majalisa ta yi matsayar kiran gwamnatin jiha da hukumomin da ke kula da harkokin ruwa da su dauki matakin da ya dace kan wadanda lamarin ya shafa.
Sani Gumbula ya ce ruwan sun yi mana barna sosai akwai bukatar gwamnati ta ba kawo mana tallafi na agajin gaggawa a gefen namu.
"Yanzu abin da nake fada maka gidajenmu da yawa sun rushe, gonaki sun nutse a ruwa sanadin wannan ibtila'i, mun yi hasara matuka, muna kira ga gwamnati ta yi abin da ya dace a kankanen lokaci, gaskiya muna cikin damuwa."