Wani dan majalisar jihar Sokoto, Hon. Aminu Boza ya fallasa inda rikakken dan ta’adda, Bello Turji yake. Hon. Boza ya tabbatar da cewa an gano dan bindiga, Bello Turji, a gabashin Sokoto da ke Arewacin Najeriya bayan shan matsin lamba daga rundunar sojojin kasar.
Rahoton Zagazola Makama ya ce ana zargin Turji ya kakaba harajin ₦25m kan wasu kauyuka da ke gabashin jihar Sokoto a Arewacin Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan Sojoji sun kai farmaki kan ‘yan bindiga a dazukan jihar Zamfara inda suka ragargaza sansaninsu da ke bayan gari. Hare-haren sojojin ƙasa da na sama sun taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yammacin kasar. An kashe hatsabiban yan bindiga kamar Kachalla Na Faranshi tare da mabiyansa a Zurmi, kuma an lalata sansanin Sani Black.
An ce dan majalisar dokokin Sokoto, Aminu Boza, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata 18 ga watan Janairun 2025 yana neman a dauki mataki. “Bello Turji yana yankin Isa da Sabon Birni na Sokoto, Har ya kakaba harajin ₦25 miliyan ga kowanne kauye.
Dan majalisar ya bukaci hukumomin tsaro da shugabannin yankin su kara kaimi wajen yaki da ‘yan bindiga, cewar Sahara Reporters.
A baya, kun ji cewa Sojojin Operation Fansan Yamma sun samu gagarumar nasara yayin da suka farmaki babbar maboyar Bello Turji a Zamfara. An ce sojojin sun kai farmakin inda suka gano makamai da harsasai, kuma sun rusa sansanin da Turji ke amfani da shi wajen shirya hare-hare. Wannan nasara ta kawo cikas ga ayyukan Bello Turji, yayin da sojojin suka kubutar da wasu mata da kananan yara da aka tsare.





