Dalilin Ziyarar Yariman Malesiya Ga Sarkin Musulmi 

Dalilin Ziyarar Yariman Malesiya Ga Sarkin Musulmi 

 

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji .Muhammad Sa'ad Abubakar ya karbi ziyarar sada zumunci da basarake kumaYariman Malaysia, tare da  Jekadan Kasar Malaysia a Najeria  da Babban Malamin su.

Tawagar Sun Samo Gagarunin Tarbo, a Filin Jirgin kasa da kasa na Sarkin Musulmi Abubakar, dake a Sokoto, sun Kuma Ziyarchi fadar Sarkin Musulmi da Hubbaren Shehu Usman fodiyo. 
Tawagar sun tattauna da wasu Manyan Malammai a kan Daular Usmaniyya.  
A ziyarar ta wuni daya sunyi Sallar Jimua a Masallacin  Sarkin Musulmi Muhammad Bello dake a Sakkwato.                     
Ziyarar na da Zimmar Kara dankon zumunci na Daulolin Musulunci na Usmaniyya da ta Malaysia. 
Ziyarar ta samu halartar Wasu Yan Majisar Mai Martaba Sarkin Musulmi, malammai da sauran su. 
Tawagar zata ziyarci Legos da Abuja dan gabatar da Mukaloli da kasidu.  
Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto