Dalilin Danbaba Dambuwa Na Barin PDP Ya Koma APC
Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba ya bar jam'iyar PDP ya koma jam'iyar APC mai mulki a Nijeriya, saboda gamsuwa da APC kamar yadda shugaban majaliar dattijai Ahmad Lawan ya bayyana.
Sanata a wata sanarwa da shugaban majalisar dattijai ya sanarda takwarorinsa a zauren majalisar ya ce Sanata Danbaba kan aiyukkan da APC ke yi a Nijeriya ne ya taba zuciyarsa ya ga dacewar ya shigo a yi tafiyar tare da shi don haka yana yi masa murna.
Bayan bayyanuwar faifan bidiyon Sakkwatawa sun yi ta tofa albarkacin bakinsu kan sauya shekar Sanata mai wakiltar Sakkwato ta kudu wasu na ganin shigowar tasa ba za ta kara komai a tafiyar APC ba, wasu na ganin za a samu cigaba duk yanda yake, ko ba komai tafiya da kari yafi raguwa.
Haka wasu magoya baya a PDP suna ganin ba a samu wata raguwa ba duk da wasu na ganin an samu gibi a cikin ficewarsa.
Wasu majiyoyi da ba a tabbatar ba sun ce Sanata Danbaba ya bar PDP ne saboda Gwamna Tambuwal ya ki amincewa da ya fito takarar Gwamna a jam'iyar PDP abin da yake ganin rashin adalci ne aka yi masa hakan ya sanya ya fice abinsa.
Duk yunkurin jin tabakin Sanata Danbaba kan lamarin ficewarsa daga PDP abin ya ci tura domin wayarsa a kashe.
managarciya