Shugaban jam'iyar APC a jihar Sakkwato da aka zaɓa a wurin babban taro na jiha wanda sunansa ya yi ɓatan dabo a lokacin bayar da takardar shedar zama zaɓaɓɓen shugaba da jam'iyar ta bayar a jihohi 34 a Abuja.
A zantawar Managarciya da Shugaban riko na jam'iyar APC Honarabul Isah Sadik Achida ya ce ba su da wani ɓangare a APC reshen jihar Sakkwato uwar jam'iyya ta ƙasa da su take hulɗa tun a zaɓen mazaɓu da ƙananan hukumomi har zuwa na jiha.
"Zan yi mamaki ka faɗi ɓangare a Sakkwato mu abin da muka sani babu gefe a jiha, APC ɗaya ce dake ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, kan maganar rashin ba mu takardar cin zaɓe hedikwata ta ƙasa ce tasan dalilin yin haka, mu bamu sani ba."
Ya ce ba wasu mutane da suka yi ƙorafi bayan kammala zaɓe a jiha domin an kare duk wata ƙa'ida da uwar jam'iyya ta gindaya a zaɓen, har zuwa baiwa sauran shugabanni takardunsu ba wani al'amari a gaban kotu tsakanin APC a Sakkwato da wasu, ba wata rigima da kowa don haka muna jiran mu ga abin da uwar jam'iyya za ta yi.
In an kira ku zaman silhu kamar yanda aka yi a Kano za ku halarta? Ya ce "a kira mu zaman silhu tare da wa, ba mu da da bangare ko rikici, dukkan wadanda aka zaba a jam'iyar nan a tare muke, ba mu ware kowa ba ana tafiya tare, in ka ce ka kira zama da wa za ka yi zaman da an ka yi mi kuma, ba mu da matsala a APC" a cewarsa.
Ya ce su ba wanda ya kawo masu kowace irin takarda da cewa yana kararsu a gaban kotu kan zaben da aka yi masu, kan sun saba doka a zaben da wakillan uwar jam'iyya da aka turo daga Abuja suka gudanar a gaban jami'an hukumar zabe. APC a Abuja bata taba kiransu kan wani korafi da wani ya kawo ba, "mu a saninmu ba mu da wata matsala ta zabe don haka nake baka tabbacin za a rantsarda mu domin cigaban APC a Sakkwato" in ji Achida.
Injiniya Aminu Ganda wanda shi ne sakataren APC a dayan bangaren da suka zabi Muhammad Mai Nasara shugaba ya ce "shugaban rikon kwarya Isah Sadik Achida ya fadi ra'ayinsa ne kawai a lokacin da aka yi zaben shugabannin jiha a wurinmu ne wakillan uwar jam'iyya suka zo a Giginya Hotal aka yi zabe suka kai sakamako na zabarmu da aka yi.
"abin da ya hana abaiwa shugaban jam'iya takardar nasarar zabe domin sun yi mana fatishin ne ga uwar jam'iya ba su aminta da zabenmu ba, hakan ya sanya shugabanni suka kafa kwamitin mutum uku domin yabi bahasin maganar kuma sun zauna da kowane bangare a gobe(Litinin) za su bayar da rahoto. Bayan nan muna da tabbacin za a ba mu takadar cin zabe a kuma rantsar da shugaban jam'iyya na jihar Sakkwato," a cewar Aminu Ganda.