Home Ra'ayi Dalilai Huɗu da ke sa rashin tsaro ke ci gaba a Sakkwato...

Dalilai Huɗu da ke sa rashin tsaro ke ci gaba a Sakkwato da Kebbi da Zamfara

31
0

Daga Dr. Kabiru Adamu

Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Beacon Security and Innovations Limited (BSIL)

Yawaitar ayyukan ta’addanci, musamman hare-haren ‘yan bindiga da sace mutane domin neman kudin fansa, ciki har da sace manyan jami’an gwamnati da aka yi kwanan nan a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, ya sake jawo hankali kan matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da addabar yankin duk da shekaru na ayyukan soji da matakan da gwamnati ta dauka.

A ranar 25 ga Yulin 2026, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Alhaji Nura Umar Abdullahi. Kasa da awanni 24 bayan haka, wasu masu garkuwa da mutane sun sace Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza na Babbar Kotun Jihar Kebbi.

Wani rahoto da kamfanin nazari da gudanar da harkokin tsaro na duniya, Beacon Security and Innovations Limited (BSIL), ya fitar ya nuna cewa matsalar rashin tsaro na kara ta’azzara a wasu sassan Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman a jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi.

Rahoton ya bayyana cewa Jihar Sokoto ce ke fuskantar mafi tsanani daga cikin matsalolin tsaro a tsakanin jihohin uku, duk da matakan da gwamnatin jihar ta dauka, ciki har da sayen motocin tsaro, kafa rundunar masu gadin al’umma ta jihar, da kuma biyan alawus ga jami’an tsaro.

Rahoton ya bukaci gwamnonin jihohin Sokoto, Zamfara da Keb wabi su kara hada kai da juna tare da inganta hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, amma kuma su tabbatar da an kafa ingantattun hanyoyin tabbatar da rikon amana da bin diddigi domin samun nasara a yaki da matsalar tsaro.

Da yake magana a wata hira da BBC Hausa, Manajan Daraktan BSIL, Dr. Kabiru Adamu, ya ce kamfanin ya sha gabatar da shawarwari masu amfani da za su iya rage yawan matsalolin tsaro idan aka aiwatar da su yadda ya kamata.
Ya ce:

“Wannan kira ne ga gwamnonin jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara. Mun lura cewa ‘yan bindiga sun kara zafafa hare-harensu a baya-bayan nan, kuma suna kara yawan yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.”

Dr. Adamu ya kara da cewa sace alkalin kotu da shugaban karamar hukuma da aka yi kwanan nan, wadanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutanen, na nuna yadda matsalar ke kara muni.

Ya ce:

“Mun san da sace alkalin kotun da shugaban karamar hukumar da aka yi, wadanda har yanzu suke hannun ‘yan bindigar, tare da hare-haren da ake kaiwa kauyuka kusan kullum.”

Rahoton BSIL ya bayyana manyan dalilai guda hudu da suke haddasa ci gaba da matsalar rashin tsaro a jihohin uku:

  1. Rashin cikakken hadin kai tsakanin gwamnatocin jihohin wajen tunkarar hare-haren ‘yan bindiga da ke ketare iyakokin jihohi.
  2. Rashin ingantattun hanyoyin tabbatar da rikon amana da bin diddigi a hadin gwiwar da ake yi da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro, lamarin da ke rage tasirin ayyukan da ake gudanarwa.
  3. Rashin aiwatar da shawarwarin kwararrun masana tsaro da za su iya karfafa matakan kariya da martani ga barazanar tsaro.
  4. Kara samun karfin guiwa da karfin aiki daga bangaren ‘yan bindiga, wadanda ke ci gaba da kai hare-hare da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Rahoton ya kammala da cewa akwai bukatar samar da cikakkiyar dabarar hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara tare da Gwamnatin Tarayya domin dakile tabarbarewar matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Dr. Kabiru Adamu na Kamfanin Beacon Security and Innovations Limited (BSIL) ya yi kira ga Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto; Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; da Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu, da su kara yin aiki tare wajen aiwatar da shawarwarin da kwararrun masana tsaro da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa ke gabatarwa domin magance matsalar rashin tsaro.

Sanya hannu:

Dr. Kabiru Adamu
Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa
Beacon Security and Innovations Limited (BSIL)

3 ga Yuli, 2026

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here