Dakatar da Zaben Kungiyar NUJ Akwai Lauje a  Nadin----- 'Yan takara

Dakatar da Zaben Kungiyar NUJ Akwai Lauje a  Nadin----- 'Yan takara
 

Daga Hussaini Ibrahim.

 

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin  Gwamna Bello  Matawallen Maradun ta dakatar da zaben shugabanin   kungiyar 'yan jarida reshen Jihar Zamfara,watau (NUJ).

 Kungiyar ta shirya  gabatar da taron ne a ranar Alhamis Mai zuwa a Gusau babban birnin Jihar Zamfara kafin dakatarwar saboda rashin tsaro.
 
Babban Sakatare na ma'aikatar yada labarai na Jihar , Barista Sani Nasarawa ya bayyana haka takarar da ya sanya hannu ya aikawa Jami'an tsaron da Uwar Kungiyar NUJ ta kasa a Gusau babban birni Jihar Zamfara.
 
 Tun da farko an shirya gudanar da zaben  a ranar 14 ga Afrilu, 2022 amma Uwar Kungiyar ta Kasa,   ta dawo da shi  baya saboda wasu dalilai zuwa ranar 12 ga Mayu, 2022.
 
 A cewar sanarwar, lokacin da aka Sanya  bai dace ba saboda matsalar tsaro da jihar ke fama da shi, inda ta kara da cewa, ma’aikatar yada labaran jihar za ta tuntubi jami’an Tsaro domin sanya rana da lokacin da ya dace domin gudanar da zaben.
 
 Haka kuma an Mika wannan takarda ga shugaban Kungiyar ta Kasa da kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara da Daraktan tsaro na jihar, da kuma Kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Kasa reshen jihar Zamfara.
 
Idan ba'a manta ba cikin mako guda an sami yawaitar kai hare hare cikin wasu Kananan hukumomi inda aka kashe mutane sama da 60, a yayin da hakan ya sanya Gwamnatin Jihar zamfara har ta kai daukin gaggawa na abinci da kudade, ga al'ummar da masifar ta shafa.
 
Wakilin mu ya tuntubi 'Yan takarar akan Dakatar da Zaben, sun bayyana masa cewa, akwai Lauje cikin Nadi dan ,'Yan takara da suka fito  Hazikai ne Jajirtatu wajan ganin 'Yan Kungiyar sun samu cigaba ta kowane bangare,Kuma sun tabbatar masu da cewa, ba za su dauki wulakanci ba daga kowane wajan tafiyar da aikin su na Jarida,Kuma Gwamanati ta makara. 
Hakan ya Sanya tayi amfani da matsala dan dakatar da Zaben.
Kungiyar da manbobinta basu wuce 200 ba, amma idan ta tashi taron ta da dubun dubatar mutane na siyasa mantawa take da Tsaro sai na 'Yan jarida.