Dakarun Sojoji Sun Yi Bajinta, Sun Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Masu Yawa 

Dakarun Sojoji Sun Yi Bajinta, Sun Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Masu Yawa 

Dakarun Sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma sun farmaki ƴan ta'adda a jihohin Sokoto da Kebbi. Dakarun sojojin sun samu nasarar fatattakar ƴan ta'addan a hare-haren da suka kai musu. 
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X. 
Sojojin sun kai hare-haren ne a ƙananan hukumomi Illela, Tangaza, Gudu, Binji, da Silami a jihar Sokoto, da Augie, Arewa, Argungu, da Dandi a jiihar Kebbi. A yayin farmakin dakarun sojojin sun kashe fiye da ƴan ta’adda 20, sun lalata sansanoninsu, kuma sun tilasta musu tserewa daga maɓoyarsu. Hare-haren waɗanda aka shirya don dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da abin ya shafa, sun sanya dakarun suna kutsawa cikin maɓoyar ƴan ta’adda a ɗazukan Tsauna, Bauni da Sarma. Dakarun sun shiga cikin maɓoyar miyagun, suka riƙa fatattakar ƴan ta’addan, suna lalata sansanoninsu sannan suka ƙwato kayan aiki. 
A ƙauyen Sarma Ruga, dakarun sojojin sun kashe ƴan ta’adda 20 a gumurzun da suka yi. Ƴan ta’addan sun tsere sun bar makamai da kayayyakinsu, waɗanda dakarun sojojin suka lalata daga baya. 
Wani babban ci gaba shi ne tsaftace ƙauyen Manja, wanda aka bar shi babu kowa har na tsawon shekaru huɗu saboda ayyukan ƴan bindiga da ƴan ta’adda.