Da Alamu Honarabul Abdullahi Hassan Zai Nemi Kujerar Dan Majalisar Tarayya A 2023

Da Alamu Honarabul Abdullahi Hassan Zai Nemi Kujerar Dan Majalisar Tarayya A 2023

 

Tsohon shugaban karamar hukumar Sakkwato ta Arewa Honarabul Abdullahi Hassan alamu na kara fitowa fili a zahiri zai nemi kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Sakkwato ta Kudu da Arewa a babban zaben 2023 a jam'iyarsa ta APC.

Honarabul Abdullahi Hassan in an dubi zubin tsarin siyasarsa za ka iya cewa ya dace ya nemi wannan kujearar, don  a cikin wadanda suka fara nuna sha'awarsu ta tsayawa takarar ma  mutum daya ne suke da da dacewa da cancanta kusan guda wanda a cikinsu ne  in har ya aminta zai tsaywa takarar APC za ta tsayar da guda, matukar ta shirya cin zaben wannan kujera da aka san amfaninta a baya sabani yanzu da wanda ke kai a majalisa yana dumama kujera ne kawai da jiran albashi.
Honarabul Abdullahi bai aiyana zai nemi wannan kujerar ba amma ganin yanda yake sakawa magoya bayansa da faranta ran na kusa da shi, alamu na nuna tayar da su tsaye ne yake yi domin su kare mutuncin kansu da mutanen Sakkwato ta Kudu da Arewa.

Da za a samu wasu mutane masu kishin kananan hukumomin nan guda biyu su sanya Abdullahi gaba har sai ya aminta da tsayawa takarar nan, da ko an taimaki al'umma ganin yanda ya shimfida aiyukka a karamar hukumar Sakkwato ta Arewa balle a ce ya samu damar da za a amince masa ya yi duk wani aikin da ya ga ya cancanta a yankinsa, lalle in dai har bai wuce gwamnansa da aiki a yankinsa ba, ba zai fi shi ba domin ba ya da abin da yake so saman yi wa jama'a aiki.

Yanda Honarabul yake ta raba alherin Babura da sauran wasu tallafi  ga matasa abu ne da yakamata a so cigaban hakan a tsaya kai da fata a mara masa baya ya wuce gaba domin kara taimakon matasa da maza da mata a wannan yankin.