Ciyamomin PDP na Jihohi 36 Sun Yanke Shawara Kan Kujerar Damagum 

Ciyamomin PDP na Jihohi 36 Sun Yanke Shawara Kan Kujerar Damagum 

Muƙaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagum ya jagoranci wani muhimmin taro da shugabannin jam’iyyar PDP na jihohi 36 a ranar Laraba a Abuja.
Wannan taro na zuwa ne a lokacin da jam'iyyar PDP ke shirye-shiryen taron majalisar zataswa (NEC) ta kasa wanda za a yi ranar 28 ga watan Nuwamba. 
Jaridar The Nation ta tattaro cewa taron ya gudana ne a hedkwatar PDP da ke Wadata Plaza a Abuja ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024. 
A wurin wannan taro, Damagum da ciyamomin PDP na jihohin Najeriya sun musanta raɗe-raɗen cewa shugaban jam'iyyar na fuskantar barazanar tsigewa.
Har ila yau, bayan taron ciyamomin jihohin sun jaddada goyon bayansu ga muƙaddashin shugaban PDP Umar Damagum.
A hira da aka yi da su, shugabannin sun bayyana babu wani abin damuwa ko barazana ga kujerar Damagum a taron NEC da ke tafe. 
A nasa jawabin, Damagum ya ce shugabannin PDP na jihohi sun kawo masa ziyara ne kamar yadda aka saba, saɓanin raɗe-raɗin da ake cewa ba su jituwa.
"Wannan taron ba sabo ba ne, dama mu kan haɗu mu tattauna a baya, ba yau ne karon farko ba, mun shirya wannan zama ne domin tattaunawa da ciyamomin jihohi. "Idan kuka duba galibin shugabannin jam'iyya na jihohi ba a daɗe da zaɓensu ba, kusan duk sababbi ne, don haka mun kira wannan zama ne mu san juna amma ba shi da alaƙa da NEC."