Cire Tallafin Mai: Tinubu Ya Tilasatawa 'Yan Nijeriya Zama Fursunonin Yaki---Matasan Kudu

Cire Tallafin Mai: Tinubu Ya Tilasatawa 'Yan Nijeriya Zama Fursunonin Yaki---Matasan Kudu

 

Gamayyar Shugabannin Matasan Kudu maso Gabashin Najeriya (COSEY) ta zargi Shugaba Tinubu kan yaudarar 'yan Najeriya da kudin tallafi. 

COSEY ta ce Tinubu na amfani da Naira biliyan biyar da ya ware na tallafi don tilasta 'yan kasar amincewa da karin kudin mai a dole. 
Kungiyar ta bukaci Tinubu ya mayar da kudin litar mai Naira 165 inda su ka ce shugaban ya mayar da 'yan kasar tamkar "fursunonin yaki", cewar Vanguard. 
Shugaban kungiyar, Goodluck Ibem ya caccaki Tinubu da damfarar 'yan Najeriya wurin amfani da kudin tallafin don tilasta musu amincewa da karin kudin mai. 
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya bai wa ko wace jiha Naira biliyan biyar da kuma tileran kayan abinci ga jihohi don rage radadin cire tallafi. Ibem ya bukaci Tinubu da ya bar daukar 'yan Najeriya marasa wayo inda ya ce ya yi amfani da matsayinsa don inganta rayuwarsu ba wai kawo wahalhalu ba.
"Yan Najeriya sun bayyana a fili su na bukatar a dawo da tallafin mai amma ya na yaudarar su da tallafin kudade da 'yan tsiraru ne za su samu. 
"Wannan karin kudin litar mai ya tabbatar cewa Tinubu bai damu da wahalhalun da 'yan kasar ke ciki ba."
Kungiyar ta kara da cewa tun farkon hawan Tinubu ya kara kudin mai daga Naira 165 zuwa Naira 530, Newstral ta tattaro.
Tinubu ya kuma kara daga Naira 530 zuwa Naira 630 inda ta ce fiye da mutane miliyan 10 sun mutu saboda wahala.