Canada Ta Yi Martani kan Rahoton Hana Hafsan Tsaron Najeriya Shiga Kasarta

Canada Ta Yi Martani kan Rahoton Hana Hafsan Tsaron Najeriya Shiga Kasarta


Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan hana hafsan tsaron Najeriya shiga Canada, ofishin jakadancin kasar ta yi magana. 
Ofishin ya ce akwai dalilai da ya sanya ta kin fayyace komai game da lamarin da ya shafi Janar Christopher Musa da wasu jami'an sojoji. 
A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Juma'a 14 ga watan Janairun 2025, cewar rahoton Tribune.
A baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa jami'an sun samu gayyata zuwa wani taro a Canada na girmama jaruman yaki, amma wasu daga cikinsu ba su samu 'visa' ba. 
Da yake magana a wani taro a Abuja, Janar Musa ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan batu, yana mai cewa wannan al'amari kira ne ga Najeriya ta tashi tsaye. 
“Wannan tunatarwa ce gare mu, mu tsaya kan kafafunmu, mu tsaya da karfinmu a matsayin kasa, mu hana a raina mu.” 
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Nuhu Ribadu, ya soki matakin Jakadancin Canada, yana mai cewa wannan abu rashin girmamawa ne ga Najeriya. 
 
Ofishin ya tabbatar da samun labarin amma ya ce ba zai yi tsokaci kan batun ba saboda dalilan tsare sirrin bayanai, cewar The Guardian. 
"Ofishin jakadancin Canada a Najeriya ya san da rahotannin da ke cewa wasu manyan jami'ai na shirin tafiya. 
"Amma saboda dalilan tsare sirri, ba za mu yi tsokaci kan matsayin neman visa na wasu ba.” - Cewar sanarwar