Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Bauchi ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa Gwamna Bala Mohammed da wasu daga cikin mukarrabansa na daukar nauyin ta’addanci, inda suka ce zargin babu tushe kuma yana da manufa ta siyasa.
A cikin wata sanarwa da shugaban CAN, Rev. Abraham Dimeus, da Sakataren ƙungiyar, Rev. Matthew Laslimbo suka sanya hannu, ƙungiyar ta bayyana cewa zargin ya kasance sharri ne da aka yi don ɓata sunan gwamnan da kuma jihar Bauchi.
Ƙungiyar ta kuma zargi cewa waɗannan ƙorafe-ƙorafen ɓangare ne na shirin abokan gaba na jihar don haifar da tashin hankali don amfanin siyasa.
CAN ta bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe, da kuma ɓatanci ga martabar jihar Bauchi, inda ta lura cewa ana ɗaukarta a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a arewacin Najeriya.
Ƙungiyar ta yi kira a yi hankali wajen gurfanar da wasu jami’an gwamnatin jihar Bauchi gaban kotu ta hannun hukumar yaki da Rashawa ta EFCC, tana gargadin cewa a kula sosai wajen gudanar da al’amarin don kada a haifar da tashin hankali.
Duk da jaddada cewa ƙungiyar addini ce ba ta da alaƙa da siyasa, CAN ta ce dole ta fito ta yi magana a matsayin ‘yan ƙasa da mazauna jihar.






